1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Baraka tsakanin kasashen Afirka a Kwamitin Sulhu

Suleiman Babayo ATB
June 19, 2020

Kenya ta samu kujera a Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya bayan fafatawa da Jibuti inda a karon farko kasashen Afirka suka fafata da juna.

https://p.dw.com/p/3e2lm
USA Übersicht UN-Sicherheitsrat | "Maintenance of International Peace and Security"
Hoto: AFP/S. Platt

Kasar Kenya ta samu kujera a Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a zabe zagaya na biyu inda ta samu kashi biyu bisa uku na kuri'un yayin fafatawa da kasar Jibuti. A zagaye na byiun Kenya ta samu kuri'u 129 yayin da Djibouti ta samu kuri'u 62. Kuma saboda annobar cutar coronavirus an yi amfani da wata ka'ida ta musamman wajen jefa kuri'ar a helkwatar majalisar da ke birnin New York na Amirka.

Wannan shi ne karon farko da kasashen Afirka suka fafata tsakanin su, abin da ake gani ka iya janyo baraka tsakanin kasashen nahiyar. Kasashen na Afirka kan tantance gwani gabanin zaben na Kwamitin Sulhu domin gabatar da kasa guda, amma a wannan karon Jibuti ta nuna rashin gamsuwa da irin wannan zaben da aka amince da Kenya tun farko. Bayan Kenya akwai kasashen Norway, Ireland, Indiya and Mexiko da suka cike zuwa mambobi 15, daga ciki kasashen biyar suka da kujeru na dindindin, a Kwamatin Sulhun na Majalisar Dinkin Duniya kuma suke da karfin hawa kujerar naki.