1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kenya: Masu bore sun sake fitowa a Nairobi

July 2, 2024

'Yan sadan Kenya sun tarwatsa masu bore a birnin Nairobi yayin da suke kokarin bazuwa kan tituna domin gudanar da sabuwar zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa.

https://p.dw.com/p/4hmjP
Kenya: Masu bore sun sake fitowa a Nairobi
Kenya: Masu bore sun sake fitowa a NairobiHoto: Monicah Mwangi/REUTERS

Masu adawa da sabbin manufofin gwamnatin Kenya sun sake fantsama kan titunan Nairobi babban birnin kasar a ranar Talata 02.07.2024, sai dai jami'an tsaro da aka baza sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zangar da ke fadar ba dadi a game da tsadar rayuwa.

Karin bayani: Ci gaba da bore a Kenya duk da cewar gwamnati ta ci tuwon fashi

Sai dai masu aiko da rahotanni sun ce zanga-zangar ta samu kauracewar kungiyar matasa ta 'Generation Z' duk da kiraye-kirayen hadakar kungiyoyin fararen fula masu yaki da tsadar rayuwa.

Karin bayani: Gomman masu zanga-zanga sun mutu a Kenya

Kawo yanzu dai wannan bore na adawa da sabon kasafin kudin kasar Kenya ya ritsa da rayukan mutane 31 a cewar kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Right Watch, sabanin adadin mutane 19 da shugaban kasar William Rutu ya bayar a ranar Lahadin da ta gabata a lokacin da yake sanar da janye sabuwa dokar.