1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Benin: Kemi Seba zai tsaya takara

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim LM
January 8, 2025

Fitaccen dan fafutukar kare 'yancin 'yan Afirka Kemi Seba ya bayyana aniyarsa ta tsaya wa takara a zaben shugaban kasar Jamhuriyar Benin, wanda za a gudanar a shekarar 2026 mai zuwa.

https://p.dw.com/p/4oxZC
Jamhuriyar Benin | Kemi Seba | Takara | Shugaban Kasa
Kemi Seba dan fafutka da ke takarar shugaban kasa a Jamhuriyar BeninHoto: Komsomolskaya Pravda/Picvario/picture alliance

Duk da cewa dan gwagwarmaya Kemi Seba ya yi fice wajen adawa da kudin CFA, amma farin jininsa ya dan ja baya a Jamhuriyar Benin da ke zama kasarsa ta asali. Seba wanda sunansa na ainihi shi ne Stellio Gilles Robert Capo Chichi ba boyayye ba ne a fagen gagwarmayar kwatar wa kasashen Afirka rainon Faransa cikakken 'yanci, duk kuwa da cewa an haife shi ne a kasar Faransan. Wannan mai fafutuka da ke da tushe da Jamhuriyar Benin da gwamnatin Faransa ta kwace takardunsa na zama dan kasarta, sunansa ya fara amo ne a kasashen Afirka tun a farkon shekarun 2000.

Bugu da kari kotuna sun yanke masa hukunce-hukunce da dama, bayan da aka same shi da aikata laifin ingiza jama'a wajen nuna wariyar launin fata. To sai dai zanga-zangar da ya jagoranta ta adawa da kudin CFA da kuma goyon baya da yake samu daga masu fafutuka na Afirka har ma da kalamai masu tayar da hankali da yake furtawa, sun janyo masa dimbin magoya baya a kafofin sada zumunta na zamani. Wadannan akidu nasa na jan hankalin matasa da dama, inda wasu suka zama magoya bayansa kamar Seth Kanlisou matashin marubucin adabi da ya bi sahun Seba wajen zama mai fafutuka.

Jamhuriyar Benin​​​​ | Patrice Talon | Shugaban Kasa
Shugaba Patrice Talon na Jamhuriyar Benin ​​​​Hoto: Bertrand Guay/AFP/Getty Images

Sai dai duk da adawa da manufofin kasashen yammacin duniya, Seba ya fara shan suka daga wasu matasan Jamhuriyar Benin da dama. Wasu daga cikinsu na danganta shi da tsattsauran ra'ayin siyasa, ko kuma mai neman bayyana wa jama'a abin da suke son ji ba tare da bayyana hanyoyin magance wadannan matsaloli ba. Diane Johnson da ta gana da Seba tun shekaru 10 da suka shude a lokacin da take karatu a jami'a, na daga cikin masu wannan ra'ayi. Wasu masu fashin baki a fannin siyasar Jamhuriyar Benin sun ce, farin jinin Seba mai shekaru 42  a duniya ya ta'allaka ne a wasu fannoni.

Amma hakikanin abin da ke faruwa a kasar Benin ya sha banbam da kamun ludayinsa, a cewar manazarcin siyasa Morgan David. Duk da cewa Shugaba Patrice Talon ya bayyana cewa ba zai sake tsayawa takara karo na uku a zaben 2026 ba, babu tabbacin cewa Seba zai iya cika sharuddan tsayawa takara. Tun bayan da aka sauya fasalin kundin zabe, ya zama wajibi wata jam'iyyar siyasa ta gabatar da takararsa kuma ya samu sa hannun 'yan majalisa ko magadan gari ko kansiloli 28 kafin a amince da takardarsa ta takara.