1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasuwanci mara shinge ya mamaye taron kolin AU

Mouhamadou Awal Balarabe
February 17, 2023

Afirka na daya daga cikin yankuna da shingayen kasuwanci ke kawo cikas ga aiki tare don gudu tare. Amma shugabannin nahiyar na amfani da taron kolin AU wajen daukar kwararan matakan habaka saye da sayarwa.

https://p.dw.com/p/4NfNI
Shugabannin Afirka a taron AU a birnin Adis Ababa na HabashaHoto: Shadi Hatem/APA Images/ZUMAPRESS/picture alliance

A yayin ganawarsu a hedkwatar kungiyar Tarayyar Afirka da ke birnin Addis Ababa na Habasha a karshen mako, shugabannin kasashe da na gwamnatocin  Afirka za su mayar da hankali kan hanyoyin a za su bi wajen habaka tsarin ciniki mara shinge a wannan nahiya. Saboda haka ne baya ga tawagogin Afirka 51, wasu kasashe da ba na kungiyar AU ba ciki har da Portugal da Spain da Qatar da Japan za su haharci taron.

Kamar yadda aka tsara, shugaban kasar Senegal Macky Sall zai mika ragamar shugabancin Kungiyar Tarayyar Afrika ga Azali Assoumani da ke zama shugaban kasar Comoros. Wannan dai shi ne karon farko da tsibirin ke jan ragamar AU bayan da Kenya ta janye takararta, inda batun fadada tsarin ciniki na bai daya kuma kara shinge a Afirka zai zama daya daga cikin abubuwan da zai sa a gaba.

Sudan | Lager des Welternährungsprogramms mit Nahrungsmittelhilfe in Darfur geplündert
Ciniki tsakanin kasashen Afirka na cin karo da kalubaleHoto: Albert Gonzalez Farran/Unamid/dpa/picture alliance

Idan za a iya tunawa dai, a shekara ta 2021 ne aka kaddamar da tsarin kasuwancin mara shinge da ya kamata ya zama mafi girma a duniya, amma kasashe kalilan ne kawai suke aiki da yarjejeniyar a karshen shekarar 2022. Alhali tsarin cinikin na da nufin inganta harkokin kasuwanci da dunkulewar tattalin arziki tsakanin kasashen Afirka. Sai dai matakin zirga-zirgar jama'a da dukiyoyi ba tare da tsangwama ba, ba ya samun goyon baya a ko'ina cikin Afirka, a cewar jami'ar diflomasiyyar Kenya Maureen Achieng, wacce a taron AU take wakilci kungiyar IGAD.

Ina aka kwana a shirin ci gaban Afirka a 2063?

Taron na 36 na kungiyar AU zai tantance matsayin shirin raya kasashen Afirka kafin shekarar 2063, in ji Ayele yayin wani taron manema labarai a Addis Ababa. Ya ce: “Shekaru goma ke nan da aka kaddamar da ajandar Tarayyar Afirka zuwa shekarar 2063, don haka lokaci ya yi da za mu tantance yadda muka yi aiki da kuma ci gaba da ajandar 2063 a cikin shekaru goma da suka gabata.” A 2013 ne kasashe mambobin AU suka tsara taswirar ciyar da Afirka gaba a cikin shekaru 50 masu zuwa. Manufar ita ce samar da bunkasar arziki a Afirka ta hanyar samun gudunmawar mata da matasa don samun ci gaba mai dorewa.

Kombo-Bild Azali Assoumani (Präsident der Komoren), Macky Sall (Präsident Senegal)
Sabon shugaban AU Azali Assoumani da tsohon shugaba Macky Sall Hoto: Kiyoshi Ota/Mast Irham/AP/picture-alliance

Aya Chebbi, wani jami'in diflomasiyyar Tunisiya kuma mai fafutukar kare hakkin mata a nahiyar Afirka, ya ce "Manufofin ajandar 2063 suna da muhimmanci kuma ya kamata a bi su da kyau. Sannan kada matasan nahiyar Afirka su manta da wadannan manufofin."