1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen duniya sun yaba da zaben Najeriya

Mohammad Nasiru AwalApril 1, 2015

Shugabannin kasashen duniya sun taya Buhari murnar lashe zaben a Najeriya kana sun yaba wa shugaba Jonathan bisa halin dattako da ya nuna.

https://p.dw.com/p/1F1YT
Mohammadu Buhari
Hoto: Ekpei/AFP/Getty Images

Tun bayan ayyana sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya da ya ba wa jagoran 'yan adawa Janar Muhammadu Buhari nasara, shugabannin kasashen duniya da masana harkokin siyasa na kasa da kasa da kuma masharhanta ke bayyana ra'ayinsu game da zaben na tarayyar Najeriya, inda suka yaba da yadda aka gudanar da zaben.

A lokacin da yake tsokaci game da sakamakon zaben na Najeriya shugaban Amirka Barack Obama ya yaba wa shugaban Najeriya mai jiran gado Muhammadu Buhari da kuma shugaba mai ci Goodluck Jonathan biyo bayan sauyin ragamar mulkin na farko tun bayan da kasar ta koma bin tsarin demokaradiyya. A cikin wata sanarwa shugaban na Amirka ya kuma bukaci Buhari da Jonathan da su ci gaba da yin kira ga magoya bayansu su mutunta sakamakon zaben su mayar da hankali wajen hadin kan kasa sannan su hada karfi don mika mulki cikin lumana.

Nigeria Abuja Mohammadu Buhari Anhänger Jubel
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Shi ma babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon bayan ya taya Buhari murnar lashe zaben da ya kwatanta wata shaida da ke nuna cewa demokaradiyya ta fara samun gindin zama a Najeriya, fata ya yi cewa zaben gwamnonin jihohi da ke tafe a ranar 11 ga watan nan na Afrilu za a yi shi cikin kwanciyar hankali da lumana.

Mataki da zai yi tasiri a Afirka

Shi kuwa ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier cewa ya yi da wannan zaben, al'ummar Najeriya sun girke wata kwakkwarar alkibla wadda za ta yi tasiri ga yankin da ma nahiyar Afirka baki daya.

Ministan ya ce bisa la'akari da manyan kalubale da ke gaban Najeriya, ya zama wajibi dukkan masu ruwa da tsaki su ba da muhimmanci ga samun nasarar mika mulki.

Manji Cheto mai sharhi ce a kamfanin Teneo mai ba da shawara kan al'amura yau da kullum birnin London ta ce Najeriya ta nuna wa duniya cewa za ta iya canja gwamnati da wani mutum da ke da kyakkyawan suna.

"Abu mafi muhimmanci ga wannan nasara shi ne, sabanin sauran shugabannin Najeriya ba a san Buhari da cin hanci da rashawa ba. Abin jira a gani shi ne ko wannan zai yi kyakkyawan tasiri a cikin gwamnatinsa da kuma wadanda za a ba wa mukami a cikin gwamnatin."

Yaki da cin hanci zai karfafa guiwar 'yan kasuwa

Ita ma kungiyar 'yan kasuwar Jamus da ke hulda da kasashen Afirka wato Afrika Verein a ta bakin babban daraktanta, Christoph Kannengießer, ya yi fatan Buhari zai yaki cin hanci da rashawa.

"Najeriya na da muhimmanci ga kamfanonin Jamus kuma shekarun bayan nan sun karfafa huloda da wannan kasa. Fatanmu shi ne sabuwar gwamnati ta kara daura damarar yaki da cin hanci da rashawa don inganta yanayin zuba jari a kasar."

Karfafa yaki da 'yan ta'adda

Nigeria Soldaten Offensive gegen Boko Haram
Hoto: Reuters/J. Penney

Su kuwa kasashen makotan Najeriya fata suka yi na cin yaki da Boko Haram. Thomas Tobin Emou dan majalisar dattawa ne na jam'iyyar CPDM da ke mulki a Kamaru ya ce babban fatansu shi ne sabon shugaban kasar ya iya shawo kan wannan matsala ta Boko Haram.

"Fatanmu na biyu shi ne kyakyawar huldar dangantakar da ta hada Najeria da Kamaru ta ci gaba da dorewa kamar yadda aka santa tun da. Don mu a gurinmu babu wani banbanci dan Najeria ne kawai aka zaba a matsayin sabon shugaban kasa kuma ya zo a daidai lokacin da kasarsa ke fama da matsalolin ayyukan ta'addanci."

Dan siyasar na Kamru ya ce abin da suke jira shi ne suka ga wadannan matsaloli sun kau a lokacin mulkin Buhari.