Shugaba Erdogan ya shirya hadewa da EU
January 12, 2021Talla
Yayin da yake jawabi ga jakadan EU a birnin Ankara, Erdogan ya bayyana fatan bude sabon babi na kawo karshen takaddama tsakanin Turkiyya da Girka bayan kwarkwaryar zaman sulhu tsakanin kasashen biyu.
Sai dai a loakci guda shugaban na Turkiyya ya kuma gargadi Girka da ta iya takunta a duk wani matakin da zai haddasa tashin hankali.
A shekarar 2015 Turkiyya ta fara tattauna yarjejeniyar shiga Kungiyar Tarayyar Turai, sai dai lamarin ya ci tura, bayan da EU ta zargi gwamnatin Ankara da yi wa tsarin dimukaradiyya karan tsaye.