Kasar Sin ta gargadi Mdd kan kasar Burma
October 9, 2007Talla
Kasar sin tace yakamata ayi taka tsantsan wajen sakawa kasar Burma takunkumi.Wannan gargadin dai yazo ne a yayin da wasu kasashe ke kiran Mdd data dauki tsauraran matakai a kann kasar ta Burma. Kasar ta Sin, wacce kawa ce ga kasar ta Burma a harkokin kasuwanci, ta kara da cewa akwai bukatar kwamitin sulhu yin karatun mun natsu, don daukar matakin daya dace akan kasar ta Burma. A dai cikin makon nan ne kwamitin sulhu na Mdd da kungiyyar Eu zasu tattauna matakin daya kamata a dauka akan kasar ta Burma. Kasar ta Sin dai na daya daga cikin mambobi na kwamitin sulhun na Mdd, wanda hakan ya bata damar hawa kujerar naki ga duk al´amarin da bai mata dadi ba.