An zargi Rasha da kin bin umarnin kungiyar NATO
January 25, 2019Talla
Cikin watan Oktobar shekarar da ta gabata ne dai, Shugaba Donald Trump na Amirka ya sanar da cewar kasar za ta yi watsi da yarjejeniyar makaman matukar Rasha ta ki bin umarnin kungiyar tsaron ta NATO kan sababbin makaman masu linzamin da ta kirkira.
Kungiyar ta NATO ta kara da cewar sababbin makaman kare dangin dai na da wuyar ganowa ta na'urori masu kwakwalwa sannan suna da nisan zangon da za su iya isa kowanne yanki a Turai cikin kankanin lokaci bayan kasancewar su cikin rukunin makamai irin na Nukiliya. Har ya zuwa wannan lokaci dai Rasha ta gaza kare kanta.