Kasar Brazil ta fada cikin rudanin siyasa
April 12, 2016
Sa'o'i 11 membobin kwamitin musamma na majalisar dokokin Kasar ta Brazil suka shafe suna ja-in-ja tsakaninsu, kafin su kada kuri'ar amince wa da ci gaba da yunkurin tsige shugaba Dilma Rousseff. 38 daga cikin 'yan majalisa 65 da ke cikin kwamitin su ne suka yi na'am da mataki na danka wa majalisar makomar shugabar kasa. 'Yan adawa na zargin shugabar ta Brazil da kin bayyana matsalar karancin kudi da kasar ta yi fama da ita a bara, da zumar lashe zaben shugaban kasa.
Sai dai a gefe guda tuni magoya bayan shugabar ta Brazil suka fara gudanar da gangami, don yin Allah wadai da abin da ke faruwa a kasar. Ko da shi ke ma tsohon shugaban kasar Luiz Inacio Lula da Silva, sai da ya dora alhakin yunkurin tsige Dilma Roussef kan kakakin majalisar dokokin Brazil.
"Su na son yi wa Dilma Rousseff juyin mulki. Sun fi mu rinjaye a lokacin da aka kada kuri'u a kwamiti musamman na majalisar. Amma wannan ba ya nufin cewar ruwa ya kare wa dan kada. Kakakin majalisa Eduarda Cunha da 'yan koransa ne suka kitsa wannan munafurcin. Yanzu dai burinsu ya cika. Amma wannan ba ya nufin cewar za su ci nasara a ranar Lahadi."
'Yan adawa sun sha alwashin tsige shugaba Rousseff
A ranar Jumma'a ce za a shigar da kudirin domin bai wa 'yan majalisar dokoki damar tafka muhawara a kan wannan batu, kafin su kada kuri'ar tsige ta, ko barinta a kan mulki a ranar Lahadin wannan mako. Sai dai hakar 'yan adawa za ta cimma ruwa ne, idan kishi biyu bisa uku na 'yan majalisa 513 da ake da su a Brazil suka kada wa Dilma Rousseff kuri'ar yankar kauna. Idan ko suka gaza samun ko da kuri'a daya ce, daga cikin 342 da suke bukata, to babu shakka shugabar ta Brazil za ta tsallake rijiya da baya.
Su ma dai 'yan majalisar dattawa suna cewar a kan wannan batu, inda daga bisani za su kada tasu kuri'a. Sai dai a wannan mataki ana bukatar rabi kuri'un 'yan majalisa ne kawai domin tabbatar da tsige Dilma Roussef. Idan ko hakan ya tabbata, to Dilma Rousseff za ta sauka daga kujerar shugabancin Brazil cikin kwanaki 180 da suka biyo bayan kada kuri'a. Shi kuwa mataimakinta ya maye gurbinta.
Carlos Marun, dan majalisa da aka zaba karkashin PMDB mai adawa, ya ce ya imanin cewar za su iya nasarar tsige Rousseff daga mukaminta.
"Daga ranar Litinin wato kwana daya baya mun kada kuri'ar yankar kauna, majalisar dattawa na da wa'adin kwanaki 10 na kada ta kada kuri'ar, tare ma da yanke hukuncin gurfanar da ita gaban kuliya. Idan aka kai wannan matsayi, to babu shakka za a sauke ta daga kan mukamin shugaban kasa, a ranar daya ga watan Mayu"
Dilma Rousseff mai shekaru 68 da haihuwa ta jaddada cewar ba wani laifin ku zo ku gani da ta aikata, wanda zai sa a tsige ta. Saboda haka ne ta danganta abin da ke faruwa da amfani da wasu dabaru na siyasa wajen neman rabata da mukaminta.