Karshen ziyarar Paparoma a London
September 19, 2010Paparoma Benedict na 16 ya kammala ziyarar yini hudu da ya kai Britaniya tare da jagorantar tsarkake wani masanin addinin addinin Kirista na karni na 19 Cardinal John Newman a Birmingham. Newman ya kasance daga cikin yan kungiyar Oxford wadanda suka dabbaka yunkurin sanya daib'un darikar Katolika a cikin tsarin mujai'ar Anglican. A ranar Asabar da ta wuce sai da Paparoman ya gana da wasu mutane biyar wadanda manyan limaman cochi suka yi lalata da su a lokacin da suke kananan yara. Paparoman ya baiyana matukar takaicinsa dangane da wannan danyen aiki wanda ya baiyana da cewa babban abin kunya ne ga cochin katolika baki daya. A waje guda kuma dubban jama'a sun gudanar da zanga zanga domin nuna bacin rai da yadda Paparoman ya tafiyar da batun tabargazar lalatar da kananan yaran.
Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala
Edita : Umaru Aliyu