Karfafa huldar Rasha da Saudiyya
December 6, 2023Shugaban na Rasha yace a da muna jiran ziyarar Mohammed bin Salman a kasarmu, amma sai gashi mun riga shi zuwa. Bayan kyakkyawar tarba da ya samu a Riyard, shugaban kasar ta Rasha ya fada cewa babu wani abu da zai iya kawo rauni a dangantakar kasashen biyu. Don haka Putin ya ce akwai matukar mahimmanci kasashen biyu su rika yin musayar bayanai kan abin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya musamman yakin da Isra'ila ke yi da Hamas. Gabanin ya isa Riyard shugaban kasar ta Rasha ya ziyarci Hadaddiyar Daular Larabawa, inda ya gana da jagoran kasar Mohammed bin Zayed Al Nahyan. Wannan ita ce ziyarar farko da shugaban kasar Rasha ya kai yankin tun bayan barkewar corona da kuma fara yakin Rasha da Ukraine. kasashen dai na matukar bukatar juna a abinda ya shafi kasuwancin makamashi da makamai.