Aikin karfafa dakarun kiyaye zaman lafiya
March 11, 2023Kasar Angola ta sanar da cewa za ta tura sojoji zuwa makwafciyarta Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma tsakanin gwamnati da kuma 'yan tawayen kasar ta ruguje. Kasar Angola dai ta kasance mai shiga tsakanin a rikici tsakanin dakarun Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango da 'yan tawayen M23, sai dai yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma da ita ya ruguje a ranar Talatar da ta gabata, wadda ke kasancewa ranar da za ta fara aiki.
A cikin sanarwar da fadar shugaban kasar Angola ta fitar, ta ce za ta girke dakarunta ne a yankunan da 'yan tawayen suka mamaye domin bayar da kariya ga fararen hula, sai dai ba ta sanar da adadin dakarun da rundunar ta kunsa ba. Gwamnatin Luanda dai ta ce ta tuntubi gwamnatin Kinshasa kafin yanke wannan hukuncin kana ta sanar wa sauran shugabanin kasashe da ma Majalisar Dinkin Duniya. Tun dai a bara ne dai kasar ta Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango ta fada cikin rikici da kungiyar M23 da ke kokarin kwace ikon yankunan kasar.