1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

090911 G7 Rezession

September 9, 2011

Abin da ya fi ɗaukar hankali a ƙasashen ƙungiyar G7 a kwanakin nan shi ne maido da yarda game da matakan farfado da tattalin arzikin duniya.

https://p.dw.com/p/12WPY
Hoto: picture alliance/dpa

Ministocin kuɗi da shugabannin manyan bankuna na ƙasashen duniya bakwai mafiya ƙarfin tattalin arziki wato G7, da ke wani taro a birnin Marseille na ƙasar Faransa suna mayar da hankali akan matakan magance koma bayan tattalin arziki a duniya baki ɗaya. Hakazalika za su kuma tattauna game da ƙarin matakan daƙile matsalolin bashi a Turai da kuma Amirka.

A kwanakin nan abu guda dukkan ƙasashen bakwai da bisa al'ada suka fi ƙarfin tattalin arziki a duniya suka sa gaba, wato maido da yarda. A wannan Juma'ar sakataren kuɗin Amirka Timothy Geithner ya rubuta a jaridar Financial Times cewa ya zama wajibi a yi duk iyawar tabbatar da cewa gwamnatoci na da ƙarfin hana sake faɗuwar tattalin arzikin duniya. Ko da yake Ba-Amirken ba ƙasarsa yake nufi ba, wato Turai yake wa hannunki mai sanda, duk da asarar kyakkyawan matsayin karɓar bashi da Washington ta yi. Za a dai buƙaci gaggauta samun amincewa tsakanin nahiyoyin biyu. A ranar Alhamis ƙungiyar haɗin kan tattalin arziki da ci-gaba OECD, ta yi kashedin cewa nan gaba kaɗan 'yar bunƙasar tattalin arziki da aka samu a ƙasashen ƙungiyar G7, za ta kau. Pier Carlo Padoan masanin tattalin arziki ne ya ce Jamus za ta samu koma-bayan kashi 1.4 cikin 100 a rubu'in ƙarshe na wannan shekara.

"Abin da muka fi gani musamman shi ne babban rashin yarda a kasuwanni da kuma fannin harkokin kasuwanci, abin da ke nuni da wasu shakku a manufofi na gajere da matsakaicin lokaci."

Frankreich Francois Baroin
Ministan kuɗin Faransa Francois BaroinHoto: picture-alliance/dpa

A wannan makon an yi ta gudanar da shawarwari a biranen Paris da Berlin game da tallafa wa ƙasar Girika da kuma kasafin kuɗin ƙasashen kansu. Ministan kuɗin Faransa mai masaukin baƙi na wannan taron, Francois Baroin, ya faɗawa majalisar dokokin ƙasarsa cewa.

"Muna tattaunawa da dukkan ƙawayenmu akan batun bunƙasar, domin samar da wata kyakkyawar manufar tattalin arziki ta bai ɗaya da zumar ƙarfafa ci-gaban bunƙasar, da samar da guraben aikin yi sannan in da hali mu biya basussukan dake kanmu."

Batun basussukan kuwa na taka rawa a gun taron musamman akan abin da ya shafi daidaita al'amuran bankuna. Ministocin kuɗi da shugabannin manyan bankunan ƙungiyar ta G7 na son su fitar da wani jerin sunayen bankuna 28 dake da muhimmanci a tsarin kuɗi, domin hana rugujewarsu ko ta halin ƙaƙa. Akan wannan batu ma ana kai ruwa rana tsakanin Turai da Amirka da kuma Asusun ba da lamuni na duniya IMF. A halin yanzu ƙasashen Turai sun nuna matuƙar rashin jin daɗin ga buƙatar da IMF yayi cewa a ƙara yawan jari a cikin bankunan Turai da kwatankwacin Euro miliyan dubu 200. Akan haka ministan kuɗin Jamus Wolfgang Schäuble ya faɗawa majalisar dokoki ta Bundestag cewa:

"Alƙalumman lissafi da Asusun IMF ya bayar game da ƙara yawan kuɗaɗen jari a bankunan Turai, wuce makaɗi da rawa ne. Za mu tattauna wannan batun a tsakanin ƙasashen G7 a taron birnin Marseille."

Bundesfinanzminister Wolfgang Schäuble
Wolfgang SchaeubleHoto: dapd

Masanin tattalin arziki na ƙungiyar OECD Pier Carlo Padoan ya ce bai kamata a bawa wata taƙaddama wurin zama ba yana mai cewa kamata yayi ministocin na G7 sun gabatar da wani saƙo bayyanan ne cewa za su iya tinkarar duk wata matsala cikin gajeren lokaci kana kuma a lokaci mai tsawo za su iya magance matsalolin giɓin kasafin kuɗinsu tare da gabatar da sauye sauye masu ma'ana. Ya ce Jamus ka iya zama abin koyi musamman saboda dangane da haramcin cin bashi da kundin tsarinta ya yi da yadda take aiwatar da sahihan matakan daidaita tattalin arzikinta.

Mawallafi: Johannes Duchrow/Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu