Ziyarar Sashen Hausa a Yprés
September 24, 2014"Na yi mamaki sosai dangane da ganin yadda aka sake gina birnin bayan da aka kammala yakin" abin da ma'aikaciyar sashen Hausa Pinado Abdu ta bayyana ke nan bayan da ta ziyarci gidan tarihin "In Flanders Fields Museum" da ke birnin Yprés na kasar Belijiyam. Sashen Hausa na DW ya kai ziyara yankin yammacin Flanders, domin tunawa da cika shekaru 100 da fara yakin duniya na farko.
A yau dai mazauna dubu 35 da ke wannan birnin na zama tamkar wani abin da aka kawata shi wanda ya samo asali daga zamanin jahiliya. Musamman babban zaure mai wata doguwar hasumiya da tsawonta ya kai mita 70, da ya kunshi gidan tarihin, wadda kuma ta kasance wata shaidar wadata ta mutanen wannan gari masu amfani da harshin Flemish. To sai dai baje kolin da ke cikin gidan tarihin ya nuna cewa babu ko daya daga cikin gine-ginen da suke nan yanzu kafin shekarar 1919. Lokacin yakin duniyar na farko, birnin Yprés ya kasance filin daga - baraguzan kasa ne kadai gurnetin Jamusawa ya bari a baya a shekara ta 1918.
Gidan tarihin na Yprés da yankin Zonnebeke da ke kusa da shi wadanda suka kasance filin daga a wancan lokacin, na amfani da hanyoyin sadarwa na zamani wajen gabatar wa maziyarta tarihin abin da ya faru tsakanin shekarun 1914 zuwa 1918. Yusuf Bala da ke aiki a sashen Hausa ya ce shi abin da ya fi ba shi sha'awa, shi ne, duk da cewa abubuwa ne marasa kyau suka faru a wancan lokacin, amma al'umma ta ajiye su a matsayin tarihi ta kuma cigaba da rayuwa. "A Afirka ba mu cika bayar da irin wannan tarihi ba, saboda haka ba mu iya yin koyi da shi" a cewar dan asalin Najeriyar mai shekaru 36 da haihuwa. "A wajenmu, a can a yankin kudu maso gabashin kasar, ko da yaushe kakanninsu na ba su labarin yadda yakin basasar da ta shafe su ya kasance, don haka mutanen wurin sun san ma'anar yaki kuma ba sa fatan sake ganin shi". Sauran yankunan kasar har yanzu ba su fahimci bala'in yakin da ya afku lokacin yakin Biafaran da ya kai tsawon shekaru 40 da afkuwa yanzu.
Bayan shekaru 100 bama-bamai na cigaba da hallaka jama'a
Ma'aikatan sashen Hausa ne suka dauki nauyin wannan tafiya na wuni biyu. Ahmed Salisu wanda ya dauki rahotanni lokacin tafiyar ne kadai DW ta dauki nauyin shi. Ya yi hirarraki da masana kimiyya da masu ziyara a gidan tarihin da ma 'yan uwansa abokan aikin da suka yi tafiya tare, kuma ya rubuta rahotanni ga tashar a harsunan Hausa da Ingilishi. "Ina so in bayyana wa masu sauraro tarihin da ke tattare da mafarin wannan yakin, mafi mahimmanci ma in kwatanta mu su irin ra'ayoyin matasan da suka ziyarci wannan gidan tarihin". Daga karshe dai matsayinsa shi ne: "Yaki abin tsoro ne".
Wannan ne ma abin da gidan tarihin na Yprés ke so ya nunar kamar yadda mai kula da gidan tarihin Piet Chielens ya bayyana cewa: "Yaki yana da munin gaske, dole ne mu nemi sulhu:" Ra'ayoyin ma'aikatan sashen Hausa ma ya zo daidai kan wannan batu "Cin zarafi, yaki da iskar gas mai guba abin da kwakwalwa ba za ta iya dauka ba ne!" A cewar Batoul Kidadi, sakatariya a sashen Afirka, ta kuma kara da cewa: "Har yanzu kuma akwai mutanen da wannan yaki ke shafa." Ma'aikatan sashen Hausa sun kadu matuka da Freddy Declerck shugaban gidauniyar gidan tarihin Zonnebeke inda ke baje kolin kayayyakin yakin da aka yi a Passchendaele a shekarar 1917, ya fada mu su cewa kowace shekara a kan gano bama-bamai, inda ba da dadewan nan ma ba wasu bama-baman da aka yi shekaru 100 da suka gabata suka rutsa da mutane biyu.
Dakarun Afirka ma ba'a manta da su ba
Daga karshen ziyarar, ma'aikatan sashen Hausan sun je makabartar Tyne Cot, wanda aka yi wa dakarun kasashe renon Ingila ko kuma Commonwealth a harshen Ingilishi. Abdourahamane Hassane wanda dan asalin Nijar ne ya ce daga cikin allunan da aka rubuta sunayen wadanda suka kwanta dama lokacin yaki har da sunan wasu 'yan Afirka "ko wadanda aka dauko su daga kasashen da aka yi wa mulkin mallaka zuwa Turai ba a manta da su ba", a cewarsa. A makabartar ne ma Ahmed Salisu ya ce "da na ga allunan da ba sunaye sai da na yi tunanin iyalan sojojin, wadanda watakila ba su san ma inda dansu yake ba. Yadda wurin yake yanzu dai ya burge sosai, ba ma yadda mutanen wadannan birane da kauyuka suka sake gina su ba, har yadda kasashen Turan suka bude iyakokinsu ga juna ya burge ma'aikatan na DW.
Ziyarar ma'aikatan sashen Hausa ta ja hankali
Ma'aikatan sashen Hausa sun ja hankali sosai, musamman ma'aikatan gidan tarihin. Suka ce ba safai 'yan Afirka ke kawo ziyara wurin ba, sun yi mamaki lokacin da suka tambayi ma'aikatan sashen Hausa dalilin wannan ziyara. Ko da shi ke a wajen rubuta sunayen maziyarta, babu sunayen Jamusawa da yawa. Ko shakka babu, a kasashen Commonwealth da Faransa da Beljiyam al'ummomi na tune da yakin duniya na farko shekaru 100 baya, fiye da al'ummar Jamus.
Da suke hanyar dawowa, ma'aikatan sun sanya hotonsu a shafin Facebook, cikin dan kankanin lokaci akalla mutane 180 suka yi tsokaci a kai. 'Yan Najeriya da dama sun danganta ziyarar da irin yakin kungiyar Boko Haram "Yanzu mu ma muna da namu yakin" wasu sun yaba wa sashen da ya kai wannan ziyara. "Muna dakon shirinku dangane da wannan ziyara" da yawa suka rubuta haka. Sakamakon dai na cikin shirinmu na "Taba ka lashe" da kuma ta Podcast.