Kammala ziyarar Ban Ki Moon a Sudan
September 6, 2007Talla
Sakatare general na mdd Ban Ki moon ya tursasawa magabatan Sudan adangane da bukatar gaggauta tura dakarun hadin gwiwa kimanin dubu 26 zuwa Darfur,da kuma daukar matakan gaggawa na kawo karshen rikicin shekaru 4 dake addabar yankin yammacin wannan kasa.
Bayan ziyara daya kai a lardin Darfur a jiya laraba,inda ya ganewa idanunsa halin da mazauna yankin ke ciki,Ban yace yanzu ne ya dada tabbatar da bukatar daukar matakai na gaggawa wajen samar da zaman lafiya a yankin,wanda ya fuskanci rigingimu dayayi sanadiyyar rayukan mutrane sama da dubu 200,baya ga wasu million 2 da rabi da suka rasa matsugunnensu.Bayan ganawarsa da magabatan kasar yau da rana nedai,Bank i Moon zai wuce kasar Tschadi,acigaba da wannan rangadi dayakeyi.