1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamfanin Shell zai biya diyya ga 'yan Bodo

Mohammad Nasiru AwalJanuary 9, 2015

Aikace-aikacen kamfanin na Shell a kauyen Bodo da ke yankin Niger Delta mai arzikin man fetir a Najeriya, ya gurbata filayen noma da kogunan kamun kifi.

https://p.dw.com/p/1EHqB
Shell Öl Umweltverschmutzung in Nigeria
Hoto: picture-alliance/dpa/EPA/Marten Van Dijl

Za mu fara sharhunan jaridun na Jamus a kan nahiyar Afirka da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung wadda a labarin ta mai taken masifar da ta addabi yankin Niger Delta ta ce:

Bayan hatsarin malalar mai da ya auku shekaru bakwai da suka wuce, kamfanin hakar mai na Shell zai biya al'ummar Bodo diyyar Euro miliyan 70. Akasarin al'ummar wannan yanki kananan manoma ne da kuma masunta. Amma man fetir daga aikin kamfanin ya gurbata filin noma da kuma kogunan da suka dogara kai wajen sana'ar kamun kifi wadda rayuwarsu ta dogara kai. Wannan diyya ta miliyoyin Euro na zama mafi yawa da aka biya a wata sasantawa a wajen kotu.

Boko Haram na kara samun galaba

Har yanzu dai muna a tarayyar ta Najeriya inda jaridar Die Tageszeitung ta buga labari mai taken kyakkyawar sabuwar shekara ga kungiyar Boko Haram, sannan sai ta ci gaba tana mai cewa.

Kimanin makonni shida gabanin gudanar da zaben ‘yan majalisun dokokin tarayya da na shugaban kasa a Najeriya, sansanin hadin guiwa na sojojin kasa da kasa da ke arewa maso gabashin Najeriya ya fada hannun masu kaifin kishin Islama. Jaridar ta ce Boko Haram ta shiga sabuwar shekara da samun gagarumar nasara sakamakon kwace wannan sansanin sojojin kundunbala da ke garin Baga bayan wani hari da ta kai kan garin da ke dab da tafkin Chadi, abin da ya tilasta mazauna tserewa don tsira da rayukansu. Jaridar ta ce ganin yadda sojoji suka ranta cikin na kare daga sansanin na Baga ya sanya zargin cewa abubuwa ba sa tafiya daidai a Najeriya. Nasarar da kungiyar ta samu a Najeriya ta biyo bayan kashi da ta sha a makwabciyar kasa wato Kamaru, lokacin da a karon farko mayakan saman Kamaru suka fatattaki ‘yan bindigar daga arewacin kasar.

Alamun nasara a yaki da Ebola a Liberiya

Liberia Ebola Versorgung
Hoto: DW/Julius Kanubah

An fara samun nasara a Liberiya inji jaridar Der Tagesspiegel tana mai cewa godiya ta tabbata ga taimakon kasashen duniya, ga alamu an fara ganin sauyi a kasar ta Liberiya mai fama da annobar cutar Ebola.

Yayin da a kwanakin nan a Saliyo aka samu yawan wadanda suka harbu da kwayoyin Ebola, a Liberiya kuwa albishir aka samu mai kuma sanya kyakkawan fata cewa ana iya dakile annobar cutar, domin a kasar ta Liberiyar inda a lokacin bazara mutane kimanin 350 suka kamu da cutar a kowane mako, yanzu an samu sauyi. A cikin makonnin karshe na watan Disamban 2014, mutane 31 ne kawai aka ba da labarin sun kamu da cuta a fadin kasar baki daya. Wannan dai alama ce cewa gagarumin taimakon da kasashen duniya ke bayarwa don taka wa cutar biriki, ya fara yin tasiri. To amma zai yi sauri a kaddamar da samun nasara kan cutar yanzu. Domin ana iya samun barkewar cutar.

Dominic Ongwen na kungiyar LRA ya shiga hannu

Ana tsare da mukaddashin Joseph Kony a Yuganda bayan ya fada hannun dakarun Amirka inji jaridar Neue Zürcher Zeitung sannan sai ta ce.

USA unterstützen Uganda bei der Jagt auf Joseph Kony
Joseph Kony na kungiyar LRAHoto: picture-alliance/dpa/Price

Mutum na biyu mafi girmar mukami a kungiyar 'yan tawayen Yuganda ta Lord's Resistance Army wato Dominic Ongwen ya mika kanshi a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Jaridar ta ce Dominic Ongwen wanda da farko aka ci zarafinsa, ya rikide ya zama mai shan jinin mutane. Shi dai kwamandan na kungiyar ta LRA na daga cikin mutanen da ake zargi da aikata munanan laifukan yaki a Afirka da aka nema ruwa a jallo.