Kamfanin MTN a Najeriya ya koka da karancin mai
May 24, 2015Talla
Ta shafinsa na Twitter, kamfanin na kasar Afirka ta Kudu na MTN wanda reshensa na Najeriya shi ne mafi girma, ya ƙara da cewar idan har cikin kwanaki biyu, bai samu man da ya ke so ba masu amfani da wannan kamfani za su shiga cikin wani mawuyacin yanayi na taɓarɓarewar layuka. Ƙasar ta Najeriya da ke fitar da gangan ɗanyan mai miliyan biyu a kowace rana, amma kuma sai ta shigo da man da take amfani da shi daga waje ta dadilin rashin matatun mai isassu a kasar, abin da masu lura da al'ammuran yau da kunlun ke danganta shi da matsalar cin hanci da rishin iya gudanar da mulki da suka yi wa ƙasar katutu.