Kamaru: Akere na kara samun goyon baya
January 16, 2018Talla
A birnin Yaounde ne dai aka girka wannan tsari da aka kira tsari na sabuwar Jamhuriyar ta Kamaru, inda a bayyane suka zabi Lawya Akere Tabeng Muna, wanda yake tsohon shugaban kungiyar lawyoyin kasar ta kamaru ne a matsayin wanda zai tsaya musu takarar neman shugabancin kasar a cewar wata sanarwa da suka fitar.
Wannan tsari dai ya kumshi kananan jam'iyyun adawa guda tara, da kuma kungiyoyin fararar hulla, cikinsu har da kungiyar nan mai suna "Now" ma'ana yanzu kenan wata sabuwar kungiyar da aka kafa ta neman sauyi a kasar ta Kamaru wadda dan takarar Akere Muna ya kafa tun bayan da ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takara a watan Oktoban da ya gabata.