1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar rashin asibiti ga matan karkara

March 3, 2020

Sakamakon rashin asibiti da cibiyoyin kiwon lafiya a yankunan karkara, mata da ke haihuwar yara ‘yan hudu na kokawa kan irin wahalhalun da suke sha yayin nakuda wanda ke  sanya su anfani da wasu hanyoyi na gargajiya

https://p.dw.com/p/3Yo9a
Nigeria Bild zum Thema Schwangerschaft | anonyme Mutter mit Kind
Hoto: DW/I. Yakubu

Sau da dama matan karkara masu juna biyu ba sa samun damar zuwa awon ciki ko gwaje-gwajen da su ka kamata domin kaucewa bari da sauran matsaloln da masu juna biyu ke fuskanta. Zainabu Mohammadu wata uwa ce ‘yar shekaru 30 wace ta saba haihuwar tagwaye  har sau uku, ta kuma sami baiwar haihuwar ‘yan hudu lokaci guda ba tare da zuwa asibiti ko taimakon ma'aikatan jinya ba. Sai dai ta ce ta fuskanci kalubale mai yawa.

Zainab ta bayyana cewa ta shafe sa’o’i  20 ta na nakuda kafin ta haifi wadannan jarirai guda 4 kuma duk a rana daya. Ta ce abin da ya sa ba ta je asibiti ba shi ne rashin kyawun hanya da kuma shiga kwale-kwale da sauran wahalhalun da mata masu ciki ke sha kafin su kai bakin kogi inda suke biyan kudin fito daganan kuma su hau babur da zai daukesu zuwa birni.

Screenshot Kaduna Frauen Paddelboot
Hanyar sufuri da kwale-kwale zuwa asibitiHoto: DW/I. Yakubu

Ta kara da cewa a kauyen makwalla da su ke zaune babu wani abisiti ko wata cibiyar kula da lafiya sai dai su na dogaro ne da wasu hanyoyi na gargajiya. Ta na mai cewa matan karkara sun fi gwammacewa anfani Ungozoma maimakon zuwa asibitin da ke da nisan gaske. Zainab ta bayyana cewa babu wanda ya yi tsammaninn za ta rayu saboda irin wahalar da ta shaka tun lokacin da ta dauki har zuwa lokacin nakudarta. Ta kce mata masu juna biyu a kauyen su na ciki mawuyacin hali.

Babu shakka rashin sufuri da hanyoyin zirga-zirgar ababen hawa da rashin gadar tsallake kogin kaduna sai ta kwale-kwale  da kuma nisan asibitin karkara zuwa birni na daga cikin manyan kalubale da matan kauyuka hayin kogi irin su Kurmin kaduna, da mashigi da makwalla da unguwar kahuta ke fama da shi

Nigeria Bild zum Thema Schwangerschaft | anonyme Mutter mit Kind
Kwale kwale domin zuwa asibiti a karkaraHoto: DW/I. Yakubu

Mallam Basiru Yusha’u shi ne maiguwar garin makwalla ya ce wasu lokutan akan samu mace ta haihu a cikin kwale-kwale kafin kaiwa asibitin birni

Tuni dai kwamishiniyar ma’aikatar mata da kananan yara ta jihar kaduna Hajiya Hafsat Baban ta janyo hankalin mata akan mahinmancin zuwa asibiti. Ta ce akwai mahinmancin gaske da ke tattare da zuwa asibiti domin za a duba lafiyar uwa da jaririnta duk a kyauta

Hafsat Baba ta kuma janyo hankalin dukkanin masu ruwa da tsaki wajen kara fargar da matan karkara akan mahinmancin zuwa asibiti maimakon zama a gida

Kiraye-kirayen mazauna kauyukan hayin kogin kaduna su ne janyo hankalin gwamnati ta gina masu Gadar tsallake rafi  da makarantar sakandare da kuma wadatasu da ababen more rayuwa.