Kalaman Cameron sun mamaye shirye-shiryen taro kan cin hanci
May 11, 2016Kasa da 'yan awoyi da fara wani taro da nufin tunkarar annobar cin hanci a tsakanin manya da kanana na kasashe, Tarrayar Najeriya ta ce taron har yanzu na da muhimmanci a gareta duk da subul da bakan mai masaukin taron kuma Firaministan Birtaniyar David Cameron, da ke nuna kasar a matsayin tungar cin hanci.
Ba dai kasafai hankali kan tashi tsakanin al'ummar Tarrayar Najeriya ba saboda batun hanci, ga kasar da ta ga fari ta kalli baki da ma rodi-rodi a harkoki na kudi can baya.
To sai dai kuma taro na birnin London a wannan Alhamis, ya dauki hankali ciki da ma wajen kasar bayan da mai masaukin bakin David Cameron ya kira sunan kasar cikin jerin na kan gaba ga batun hancin a duniya.
Akalla shugabannin kasashe 50 ne dai aka tsara za su kasance a birnin da nufin nazari da ma hanyar tunkarar annobar da ke zaman barazana mafi girma ga kasashe matalauta.
Muhimmin taro ga Najeriya
Kamin kalaman Cameron din da ake yi wa fassara iri dabam-dabam a ciki da ma wajen kasar. Duk da cewar dai da yawa sun yi fushi ga gwamnatin kasar taron na da muhimmanci kuma hukuncin da ke shirin bin baya ma na da muhimmanci a fadar Mallam Garba Shehu da ke zaman kakakin shugaban Najeriya.
"Gudunamawa da nasarori da shugaban Najeriya ke samu a yaki da cin hanci da rashawa na daga cikin dalilan da suka sa aka gaiyace shi wannan taro. Kuma a jawabin da zai yi ana sa rai kasashe da ke da matsaloli irin Najeriya za su iya kwaikwayo da matakan da sabuwar gwamnat ke dauka bisa manufar yaki da cin hanci da rashawa."
Barawo na zaune ko kuma mallam Mamman dai ko bayan gwamnatin kasar da ke birnin London da nufin neman hanyar dawo da kudi, wasu na kallon kalaman Cameron din a matsayin kokari na tallata taron ga duniya a tunanin Dr. Emman Shehu da ke zaman babban darakta ga cibiyar horar da jaridu da ke a birnin Abuja.
Fatan cimma yarjeniyoyi masu amfani
Talla ga mai saye ko kuma kokari na bacin suna dai, Tarrayar Najeriya da kawayenta na fatan kaiwa ga cimma jerin yarjeniyoyin da suka tanadi dawowa da kudade da ma hukunta masu laifin sata a ko ina. Abun kuma da a cewar Hon. Ahmed Babba Kaita da ke zaman dan majalisar wakilai ta kasar ya sanya taron ke zaman da muhimmanci ga kasar komai daci.
Abun jira a gani dai na zaman tasirin taron da ke zuwa a daidai lokacin da wata jaridar birnin London ke cewar akwai kadarorin sata ba adadi cikin kasar ta Birtaniya da aka dauko daga kanana na kasashe irinsu Tarrayar Najeriyar.