Kaduna: Sana'ar ba da hayar kwale-kwale
September 18, 2019A wani mataki na rage zaman banza da samarwa kai abin yi da kuma rage dogara da mazajensu, wasu mata a wani kauye da kem a Kaduna sun rungumi sana'ar ba da hayar kwale-kwale da ake amfani da su wajen daukar fasinjoji da kuma jigilar kayayyaki don kaiwa cikin. Wannan sana'ar dai na sama musu dan abin da suke biya wa kansu bukatunsu na yau da kullum da shi.
Matan dai suke ba da kudaden kera wadannan kwale-kwalen kamar yadda Habiba Abubakar dayya daga cikin matan ta yi karin haske.
"Abin da ya jawo hankilana kan kera wadannan kwale-kwale muna ba da haya shi ne saboda mu taimaka wa mazajenmu domin yanzu ruwa ta yi karfi. Dole ne a hada karfi da karfe domin a kashe mahaukacin kare."
A da dai kudin buga kwale-kwale a cewar matan, Naira dubu 12 ne amma yanzu ya kai Naira dubu 23 saboda tsadar kayakin aiki. Duk da haka dai matan sun ce suna samun abin rufin asiri musamman na taimaka wa iyalansu wajen daukar dauniyar yau da kullum musamman ta yara.