1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kaduna: Nakasassu masu sana'a na korafi

November 20, 2018

A jihar Kaduna da ke Najeriya masu bukata ta musamman wadanda suka daina bara suka rungumi sana’o'i, sun koka a kan yadda gwamnati da al’umma ba sa sayen kayayyakin da suke kerawa.

https://p.dw.com/p/38aSt
Behinderte in Arika - Rollstuhlfahrer
Hoto: picture-alliance/dpa

A jihar Kaduna a shekarun baya-bayan nan dubunnan nakasassu ne suka yi watsi da bara tare da kama sana'o'i musamman na hannu da nufin samar wa kansa na saka baki salati. Wasu daga cikin nakasassun da suka zamo abin misali a jihar ta Kaduna sune rukunin nan na wasu guragu kimanin 20 wadanda suka kafa wani kamfanin aikin walda na kera kyauraye da kekunan guragu. Sai dai Musa Abdullahi daya daga cikin guragun da ke aiki wannan kamfani ya yi zargin gwamnati da mutan gari na kyamatar sayen kayayyakinsu:

"Akwai mutanen da za su jefe ka da wata magana ta kyama wacce za ka jima kana tunaninta, sannan kuma ya ki sayen kayanka, sannan idan ka bar aikin ka koma bara sune za su ta fadin bakaken maganganu kanka"

Djibril Imorou
Hoto: DW/M. Dronne

Irin wannan kyama a cewar wadannan guragu ta yi muni yadda sai su yi watanni uku  ba tare da an zo an sayi kekunan guragu da suke kerawa ba. To sai dai kuma ko baya ga guragu ne suma makafi wadanda suka yi watsi da bara tare da rungumar sana'a na korafi da yadda jama'a ke dari-dari wajen sayen kayayyakinsu. Ibrahim Makaho wanda ke aikin saka abubuwa da dama na daga cikin amsu irin wannan korafi:

"Ina saka kwandon da ake zuba takardar katse ba haya, ko kuma ta gugar kura a cikin mota, ko kuma wani datti na hannu. To sai dai ba kasafai mutane ke zuwa su saye ba, sun fi amfani da wanda ake kerawa a kamfani"

A shekara ta 2015 ne dai gwamnan Kaduna Nasiru Elrufai ya haramta wa masu bukata ta musamman yin bara a jihar Kaduna. To sai dai a yanzu za a iya cewa wadannan kalubalai na rashin samun ciniki na kayayyakin da nakasassun ke kerawa na kokarin mayar da hannu aagogo baya a game da ci-gaban da aka samu wajen raba nakasassun da bara a jihar ta Kaduna.