1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bulo da na'urar auna ruwan fanfo a Kaduna

October 23, 2019

Wani matashi a Kaduna ya kirkiro na'urar da za ta rinka auna adadin ruwan fanfo da mazauna birane ke sha a kowane wata. Matashin dai ya karanci kimiyyar halittu ne a jami'a amma kuma ga shi yanzu ya zama tamkar injiniya.

https://p.dw.com/p/3Rlhn
Pumpe zur Wasserversorgung Afrika
Wannan wani tsohon hoto ne da muka yi amfani da shiHoto: Imago/Peter Udo Maurer

Shekara guda matashi Hamza Yunusa mai shekaru 29 tare da wani abokinsa suka kwashe suna kokarin kirkiro wannan na'ura. Burin su Hamza dai shi ne gwamnatocin jihohi su yi amfani da wannan mita wurin kayyade adadin ruwan famfo da magidanta ke sha, ma'ana dai na'urar na aiki kamar yadda mitar lantarki ta ke aiki. Hamza dai ya tabbatar da cewar sun sayi dukkanin kayayyakin hada na'urar a cikin Najeriya kuma bisa bincikensu a duk fadin kasashen Afirka babu wata kasa da a yanzu take amfani da irin na'ura mai kayyade ruwan fanfo.