HdM: Matashi mai yi wa itatuwa aure
June 9, 2021Itatuwan da matashin ke kulla musu aure dai, sun hadar da lemo da mangoro da gwaiba da gwanda da sauran itatuwan kayan marmari. Ya kuma kama wannan sana'ar gadan-gadan, inda yake yi wa dubban itatuwa aure. Matashi dai ya fara wannan sana'a, bayan samun horo na wata guda daga wani kwararren masanin halittu da tsirrai, a kan hanyoyin amfani da sababbin hikimomin zamani na auren itacen marmari. Matashin mai suna Ibrahim Salihu ya ce sana'ar auren itacen kayayyakin marmarin na da matukar fa'ida da a irin wannan yanayi.
A cewarsa yana yi wa itatuwan kayan marmari sama da dubu 70 aure a kowace shekara, kama daga na gargajiya zuwa na zamani. Yace abun da ya kamata a sani a kan auren itacen marmari ,shine ana yanke kan kamar yadda ake yin kaciya,sannan sai a kowa. Daga Nasarorin da ya samu dai, akwai na yadda yake samun na rufin asiri da kuma yadda yake horas da matasa sana'ar. Sai dai ya ce batun tabarbarewar tsaro da rashin tallafi na daga cikin manyan kalubalen da ke ci-masa tuwo a kwarya.