Himma dai Matasa: Bai wa manoma horo
March 4, 2020Matashin kuma kwararren masani kan sauyin yanayi da ya kammala karatunsa na jami'a ya koma bai wa manoma horo kan sababbin dabarun noma na zamani don tunkarar kalubalen sauyin yanayin, kama daga barazanar kwararowar hamada da fari da ambaliya da suke haifar da karancin albarkatun gona. Matashin mai suna Muhammad Zakariyya ya bayyana cewa yana yin wannan yunkurin ne domin kawo karshen matsalar karewar wasu tsirrai da ma bunkasa samar da amfanin gona.
Zakariyya ya kara da cewa ya samu gagarumar nasara tun bayan da ya fara bai wa manoma horo kan yadda za su inganta nomansu ta la'akari da sauyin yanayi da ma yadda za su kare gonakinsu daga fadawa halin tasku a lokacin da suka yi kicibis da fari ko kuma ambaliya. Ya ce za a iya cimma gagarumar nasarar kawo karshen kalubalen matasalar karancin abinci da kwararowar hamada da fari ko kuma ambaliya, in har manoman suka fahimci abin da ake nufi da sauyi ko kuma dumamar yanayi tare da yadda da illolinsa, kamar yadda yake kokarin ba su horo da wayar musu da kai dangane da wannan matsalar.