Matasa da ke cinikin kwadi a Kaduna
September 11, 2019Talla
Matasa masu yawa ne a wata unguwar ta Kaduna da ake kira da sunan Gwari suka yi watsi da wasu kananan sana’o’in hannu da suke yi domin rungumar sana’ar kamun kwadi da suke samun makudan kudade a kowace rana. Sana’ar dai a cewar shugaban matasan Felix Peter na bunkasa a arewacin Nigeria sakamakon yadda wasu kabilun ke bukatar naman kwado da kuma yadda ake magani da bangaren jikinsa.