1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kaddamar da yakin neman zabe a Najeriya

Uwais Abubakar IdrisJanuary 6, 2015

Hukumar zaben kasar watau INEC ta fitar da kundin doko da'a ga jam'iyyu, wanda ake zaton zai iya yin tasiri wajen wanyewa lafiya.

https://p.dw.com/p/1EFrQ

To zaryar kaiwa ga madafan iko da jam'iyyun siyasun Najeriyar suka fara gadan-gadan a yanayi na yada kanin wani da aka fara gani zahiri, biyo bayan kadammar da yakin neman zaben kasar, na zama abin da ake murna tare da yake na dar –dar din ganin an wanye lafiya.

Wannan ya biyo bayan dumamar da yanayin siyasar Najeriya yayi da ya sanya hukumar zaben Najeriyar fitar da ka'idojin da'a ga yadda take son jam'iyyun su gudanar da yakin neman zabensu ta hanyar kauwacewa shagube, habaici da ma zargin juna, da ka iya tunzura magoya bayansu. To ko me yasa hukumar zaben tafi baiwa batun rage amfani da kudi fifiko a yakin neman zaben? Mr Nick Dazan shine mataimakin darakta yada labaru na hukumar zaben Najeriyar.

Abinda yasa ai huruminmu shi ne mu yi wa kowa adalci kuma mu tabbatar da cewar wani dan takara ko wata jam'iyya bai fi wani ba, shi yasa in aka duba sashi 91 na dokokin zabe aka cewa wanda zai yi takarar shugaban kasa bai kamata ya kashe fiye da bilyan guda ba, kuma duk wanda zai bashi taimako ko tallafi bai kamata ya bada fiye da milyan guda ba. Amma abinda muke gani ko muke karantawa ya sabawa wannan doka.

Wahlen Nigeria Attahiru Jega
Shugaban INEC Attahiru JegaHoto: AP

Koda yake fitar da ka'idojin da'a ga yakin neman zaben da aiki da shi batutuwa ne guda biyu masu wuyan sha'ani a tsari irin na Najeriya. Ko yaya zasu tabbatar da jam'iyyun sun yi aiki da shi musamman ganin yanayin siyasar ya dau dumi? Dr Yunusa Tanko shugaban majalisar jam'iyyun siyasun Najeriyar da suka rattaba hannu a kan kundin.

Eh Alhamdulillahi ya dau dumi amma abin tamabaya ya ya kamata a yi shi, abinda ya addabi ‘yan Najeriyai shi ya kamata a fuskanta, maganar abinda ya damu mutane irin rashin aikin yi, asibiti shi ne ya kamata a maida hankali a kai, ba wai zage-zage ba. Kuma muddin aka yi haka to mutane zasu ce wadannan suna da alkibla, to ka ga duk wani tunani na fadace fadace da wani ke da shi zai kau da shi.

A lokutan baya dai kananan jam'iyyun kan yi koken ana masu babakere da ma nuna masu fin karfi kama daga amfani da kayan gwamnati irin su kafofin yada labaru da filayen gudanar da taro ga jam'iyya mai mulki su kuwa a barsu ko oho. Abin jira a gani shi ne ko za ta canza zani a wannan shekara domin kamanta adalci shi ne mafita ga yanayin na Najeriya.