Juyin mulkin soja a Sudan ya ja hankalin jaridun Jamus
October 29, 2021Jaridar Neue Zürcher Zeitung, ta ce sojojin sun ji tsoron kada a dora masu alhakin laifukan da suka yi a baya, ta yadda za su rasa hanyar da suke yin facakarsu. Jaridar ta kara da cewa sabon mai rike da ikon kasar wanda ba kuma sabo ba ne ya debo ta dayawa. Jagoran sojojin Janar Abdelfatah Burhan, tun bayan juyin mulkin da ya kifar da gwamnatin Albashir shekaru biyu da suka gabata, shi ne ke juya al'amura. Daga karshe ya kama firaministan rikon kwarya da ya fito a bangaren farar hula kana ya yi masa daurin talala, kafin a sake shi. Burhan ya dauki mataki mafi hatsari tun bayan kifar da gwamnatin Albashir a baya, domin da tuni har kasar ta fara maido da kyakkyawar hulda da kasashen yamma wadanda ke kokarin ganin an gudanar da zabe sahihi.
Tasirin rundunar kiyaye zaman lafiya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta yi sharhinta ne bisa hirar da ta yi da ministar harkokin wajen Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya Sylvie Baïpo Temon. Tambayar fako ta jaridar ita ce, shin anya akwai tasirin rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Bangui? Domin kuwa tun shekara ta 2012 kasar ke cikin yakin basasa tsakanin mayakan wannan kabila izuwa wancan sai kuma 'yan bindiga da ke yaki da gwamnati. Ita kuwa ministar harkokin wajen sai ta mamsa da cewa abun kaito shi a zahirance dai bama ganin tasirin rundunar ta Majalisar Dinkin Duniya sai ma akasi, domin kungiyoyin mayaka ke fada gwamnati sai kara samun makamai suke yi, aikata laifuka sai karuwa yake yi. Don haka tace tabbas akwai hadin baki tsakanin kungiyoyin 'yan tawaye da rundunar Majalisar Dinkin Duniya wace aka sani da MINUSCA.
Makomar yaki da ta'addanci a yankin Sahel Jaridar Die tageszeitung, ta fara sharhinda cewa gomma mu sasanta da su maimakon mu nemi murkushesu. Jaridar na magana ne kan kasar Mali, wace yanzu ita ma kamar Burkina Faso ta dau matakan sasantawa da 'yan ta'adda maimako cigaba da yakarsu. A Burkina Faso arewacin kasar ya kasance a cike da tashin hankali wanda mayaka suke haddasawa a kan iyakarsu da Mali, inda kimanin 'yan Burkina miliyan daya da rabi suka rasa gidajensu ya yinda yanzu suke yin hijirar da rai a kudancin kasar har zuwa kasar Cote d'Ivoire abinda yasa gwamnati ta fara neman sasanci, ya yinda a yanzu makobciyarsu Mali ita ma ta faraneman sasanci maimakon amfani da karfin soja.
A karon farko Burundi ta samu alluran rigakafin Corona Jaridar Neue Zürcher Zeitung, wace tace a Burundi da ke zama kasa ta uku kacal a duniya da basu samu allurar riga kafi ko daya ba, amma makon jiya alluran farko sun isa. Jaridar ta ce 'yar mitsitsiyar kasar da ke gabashin Afirka da ke fama da bakin talauci, ta samu maganin ne, bisa taimkon da China ta yi, inda China ta bata kyautar allurai miliyan daya da rabi. Kasar Burundi tun da aka fara cutar ta bada rahotannin kamauwar muta ne 7000 yayinda 45 suka mutu sanadiyar cutar. Dama dai kasashe uku ne kacal a duniya suka rage wadanda basu karbi alluarar riga kafin COVID-19 ko daya ba, wato bayaga Burundin akwai kasashen Eriteriya da Koriya ta Arewa.