Jonathan ya sallami ministoci tara
September 11, 2013Ministocin da guguwar ta kai ga tankadar da su dai sun hada da ministan tsara tattalin arzikin tarrayar Najeriya Dr Shamsudeen Usman, da 'yar uwarsa dake kula da muhalli Hajiya Hadiza Mailafiya. Sai kuma Farfesa Rukaiyatu Rufai dake zaman tsohuwar ministar ilimin kasar.
Hajiya Zainab Ibrahim Kuci dake zaman karamar ministar wutar lantarkin kasar ta Najeriya mai dai an yi waje-road da ita, haka ma Olugbenga Ashiru da kafin wannan garambawul yake zaman ministan harkokin wajen kasar, da Farfesa Ita Bassey Ewa dake zaman ministan kimiyya da fasaha yayi gida, haka ma karamin ministan harkokin noma Alhaji Bukar Tijjani.
An kuma raba Ms Amma Pepple da mukaminta na ministan ginin gidajen kasar sannan aka shaida wa karamar ministar tsaron kasar Eerelu Olusola Obada ta je gida don hutu.
Garambawul don daidaita sahu
Ana dai ta'allaka kokari na dorin saiti na gwamantin a fadar ministan yada labaran kasar Labaran Maku a matsayin babbar hujjar juyin dake zaman irinsa na farko ga gwamantin da kuma har yanzu 'yan kasar ke jiran ganin alkawarin sauya rayuwarsu cikin tsarin ta:
Babu dai ko da aiki daya tilo a cikin kusan 350 din da gwamantin kasar ta kai ga bada kwangilarsu a shekarar bara ne dai aka kai ga tabbatar da kammaluwarsu zuwa watan satumban da muke ciki; a wani abun da ke zaman alamu na gazawar gwamantin da sannu a hankali take kara fitowa fili cewa ta gaza cikin mafi yawan alkawura na sauya rayuwar al' umarta.
To sai dai kuma ko bayan nan tuni an fara ambato batu na tasirin rikicin cikin gidan jam'iyyar PDP mai mulki a cikin sauyin da ya kalli akalla ministoci 4 daga jihohin gwamnoni hudu 'yan sabuwar PDP sun rasa aikinsu.
Tuni dai da ma minista na biyar kuma na jihar Sakkwato ya kai gida sakamakon matakin gwamnatin a wani abun da ake wa kallon kora da kara bisa rawar 'yan biyar na gwamnonin jam'iyyar.
Babakeren 'yan siyasa
Akwai dai masu kallon sabon sauyin a matsayin kokarin sauya majalisar ministocin da ke da rinjayen 'yan boko ya zuwa ga mai babakere na siyasa ga shugaba Jonathan da ke kara kusantar sabon zabe a cikin halin rudani da rashin tabbas.
To sai dai kuma a fadar Makun babu siyasa ba kanshinta cikin sauyin da 'yan Najeriya suka share tsawon lokaci suna fatan gani cikin kasar.
Ana dai sa ran mafi yawa na ministocin da za su zo kowane lokaci cikin makon gobe a matsayin majalisar da za ta jagoranci yakin tabbatar da burin sake cigaban mulkin kasar a bangaren shugaban da ke tsakar ruwa kuma ke neman igiyar kamawa zuwa tudun mun tsira.
Majiyoyi ma dai sun ce shugaban na shirin zabe daga goggagu na 'yan siyasa ta kasar domin fuskantar rikicin gwamnonin da ma kila tabbatar da kishiya cikin rikicin da ke barazana ga karfin jam'iyyar a jihohinsu.
Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Mohammad Nasiru Awal