1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jonathan ya lashe zaɓen shugaban ƙasa

April 19, 2011

Jam'iyyar PDP ta lashe zaɓen shugabancin Najeriya a karo na huɗu a jere, abinda ke nuna cewa jam'iyyar za ta yi shekaru 16 tana jan ragamar mulkin ƙasar, ka na da rinjayen 'yan majalisar dokoki a majalisar Tarraya.

https://p.dw.com/p/10vx5
Masu zabe a NajeriyaHoto: dapd

Shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan, wanda hukumar zaɓen ƙasar ta ayyana a matsayin ɗan takaran da ya lashe zaɓen shugaban ƙasar wanda ya gudana a ranar Asabar da ta gabata, ya yi ƙira ga 'yan ƙasar da su zauna lafiya da juna da kuma mantawa da bambancin siyasar da ke tsakanin su. Shugaban ya bayyana hakan ne bayan da tashe-tashen hankula suka ɓarke a wasu biranen arewacin ƙasar yankin da jam'iyyar adawa ta CPC ta fi ƙarfi, bisa zargin tabka maguɗi a sakamakon zaɓen. Tuni dai masu sharhi akan harkokin Najeriya suka bayyana taƙaicin su ga yanayin da ƙasar ta shiga bayan zaɓen shugaban ƙasar, abinda Dakta Husseini Abdu dake rajin inganta dimoƙraɗiyya a ƙasar ya ce akwai buƙatar shawo kan sa nan take, domin gudun shiga ruɗani.

Sakamakon zaɓen dai ya nuna cewar Jonathan ya sami ƙuri'u sama da miliyan 22, a yayin da mai binsa a baya kana tsohon shugaban ƙasar Janar Muhammadu Buhari kuwa, ya samu ƙuri'u miliyan 12 da 'yan kai, abinda ya nuna cewar shi Jonathan ya sami kaso 57 cikin 100 na ɗaukacin ƙuri'un da aka kaɗa, a yayin da Buhari kuma ya tashi da kashi 31 cikin 100 na ƙuri'un. Sai dai kuma ɗaukacin jam'iyyun adawa a ƙasar sun yi watsi da sakamakon.

Sauti a ƙasa

A ƙasa kuna iya sauraron sauti, cikin rahoto kan sakamakon zaɓen da hukumar INEC ta bayar da kuma hira da masu sharhi kan al'amuran siyasa wato Husseini Abdu, bisa abinda ya biyo sakamakon zaɓen, kana da rahoto kan yadda zaman lafiya ya dawo a Sakwato, bayan tashin hankalin da aka samu jiya

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Usman Shehu Usman