Jonathan ya ki yi wa 'yan Boko Haram afuwa
March 7, 2013Daga saukar Shugaban a garin Damaturu inda aka tsaurara matakan tsaro tare da takaita zirga-zirgar mutane a cikin sa, ya fara kai caffar ban girma ga Sarkin Damaturu Ba Shehu Umar Ali Ibn El-Kenemi. Daga nan ne kuma shi da tawagar sa suka wuce fadar gwamnatin inda ya gana da masu ruwa da tsaki a jihar tare da jin korafe-korafen su ciki kuwa har da na tsohon gwamnan jihar Senata Bukar Abba Ibrahim.
Dukkanin alamu dai sun nuna cewa babu wani rubutaccen sako da shugaban ya je da shi garin don gabatarwa al'umma.Maimakon haka ma dai ya mai da jawabi tare da kare gwamnatin sa game da irin korafe-korafen da al'umma suke yi dangane da yadda gwamnatin sa tayi watsi da yankin da rikici da gurgunta. Dangane da bukatar da aka gabatar na neman yi wa ‘yan kungiyar Jama'atu Ahlussunah Lidda'awati wal jihad da aka fi sani Boko Haram Afuwa, Jonathan ya ce ba za ta yiwu ba.
"Ba'a yin Afuwa ga wadanda ke ayyukan su a boye, ‘yan Boko Haram suna aikace-aikacen su ne a boye don ba wanda zai fito ya bayyana kan sa cewa shi dan Boko Haram ne ,sabanin yadda aka yi a yankin Niger-Delta inda in ka nemi Shugabannin za su zo ku zauna da su. Saboda haka babu maganar yin Afuwa a yanzu ga ‘yan Boko Haram."
Yadda al'uma suka dauki matakin Jonathan
Wannan sako bai yi wa da dama daga cikin mahalarta wannan taro dadi ba kamar yadda fuskokin su ya nuna ganin a baya sun yi fatan shugaban zai yi amfani da wannan dama na ziyarar ta sa wajen sanar da shirin yin Afuwa ga masu gwagwarmaya da makaman. Da yawa daga cikin al'ummar jihar Yobe ba su yi marhabin da wannan ziyara ba musamman ganin babu wani sako na musamman da shugaban ya je da shi, ga kuma mummunar takurawa da suka ce an musu ta hana fita ko don neman na sawa a bakin Salati.
Wannan ziyara ta shugaban Jonathan dai wacce aka ka watsa kai tsaye a gidan talabijin na kasar ta sha suka daga bangarorin al'ummar yankin, ganin irin jinkirin da aka samu na tsawon shekara hudu ana rikici a yankin amma bai taba takowa ko kuma yin jaje bare aikewa da gudumawa ba.
Rahoto cikin sauti na kasa
Mawallafi: Al-Amin Suleiman Mohammad
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe