Jonathan ya kai ziyarar ta'aziyya a birnin Katsina
May 8, 2010Shugaban Nijeriya Dakta Goodluck Jonathnan ya ziyarci Iyalan marigayi shugaban ƙasar Malam Umar Musa 'Yar'adua a birnin Katsina dake yankin arewacin Nijeriya, domin nuna juyayin sa bisa mutuwar tsohon shugaban. Daga cikin mambobin tawagar shugaban ƙasar a lokacin ziyarar dai, harda Uwargidar sa Patience Jonathan, da sakataren gwamnatin tarayyar Nijeriya Alhaji Mahmud Yayale Ahmad, da kuma gwamnan jihar Katsina Alhaji Ibrahim Shehu Shema, inda ya yi alƙawarin ci gaba da gudanar da kyawawan ayyukan da 'Yar'adua ya faro.
A halin da ake ciki kuma wasu tsoffin shugabannin Nijeriya ukku, sun yi kira ga shugaba Goodluck Jonathan na ƙasar, daya ɗauki matakan da suka dace wajen tabbatar da cewar, an gudanar da zaɓukan ƙasar - baɗi idan Allah ya kaimu cikin adalci. Janar Yakubu Gowon, wanda ya jagoranci tawagar tsoffin shugabannin data gana da Goodluck Jonathan ya shaidawa manema labarai bayan ganawar cewar, yana fata shugaban ƙasar zai mayar da hankalin sa wajen ganin an gudanar da zaɓe mai nagarta a Nijeriya a shekara ta 2011. A cewar janar Gowon, abinda kowa ya zura ido ya gani shi ne gudanar da zaɓukan dake tafe - cikin 'yanci da walwala. Tawagar dai, ta ƙunshi Alhaji Shehu Uthman Aliyu Shagari, da kuma Cif Ernest Shonekan, waɗanda dukkan su tsoffin shugabannin Nijeriyar ne.
Wata sanarwar data fito daga fadar shugaban Nijeriya bayan ganawar, ta bayyana cewar, shugaba Goodluck Jonathan ya shaidawa tsoffin shugabannin ƙasar cewar, babban abinda ke gabansa shi ne nunawa 'yan Nijeriya da kuma al'ummar ƙasa da ƙasa cewar, Nijeriya za ta iya gudanar da sahihin zaɓe.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Halima Balaraba Abbas