1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jonathan ya kaddamar da takarar tazarce

September 18, 2010

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya kaddamar da takarasa a zaben 2011

https://p.dw.com/p/PFmT
Shugaba Goodluck JonathanHoto: AP

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan a ranar Asabar din nan ya ƙaddamar da aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin ƙasar a zaɓe mai zuwa na 2011. Da yake jawabi ga taron magoya baya da suka hallara a dandalin Eagle Square a Abuja, Jonathan ya ci alwashin haɗa kan yan Nigeria a saboda haka ya bukaci jama'a su kaɗa masa ƙuri'a a lokacin zaɓe. "Yace na zo in shaida muku dukkan ku yan Najeriya cewa Goodluck Ebele Azikiwe Jonathan shine mutumin da ku ke bukata".

Tun dai a ranar Larabar da ta wuce shugaban ya sanar a shafin Facebook cewa zai fito takarar zaɓen da za'a gudanar a watan Janairu, yayin da ake cigaba da jayyaya a Jam'iyarsa ta PDP a game da ko za su ba shi goyon baya ko kuma za su tsayar da ɗan takara daga arewacin ƙasar. Taron dai ya sami halartar gwamnonin jihohi da dama da Ministoci da kuma´yan majalisar dokoki.

A waje guda a ranar Asabar din nan ce itama jam'iyar adawa ta ANPP ta ke gudanar da babban taronta a Abuja domin zaɓar sabbin shugabanni da za su ja ragamar jam'iyar bayan ƙarewar wa'adin tsoffin shugabanni ƙarƙashin jagorancin Chief Edwin Umeh Ezeoke.

Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala

Edita : Yahouza Sadissou Madobi