Jonathan ya cika shekara guda kan kujerar mulki
May 29, 2012Ra'ayi na shan bambam a tsakanin jami' an gwamantin Najeriya da ke cewar ta yi ruwa tana shirin yin tsaki a makomar kasar da kuma 'yan adawar da ke cewar mu gani a kas in ji kare.
An dai kira asibiti an kuma ambato takin zamani, an mace an gyara jirgin sama da na ƙasa da ƙoƙarin inganta harkokin ruwa to sai dai kuma daga dukkan alamu an gaza kaiwa ga burge 'yan adawar tarrayar Najeriya da suka ce basu gani a ƙasa ba, game da bikin cika shekara guda na gwamantin shugaba Goodluck Ebele Jonathan.
Duk da cewar dai a bana babu kiɗa da rawa irin na al'adar wannan lokaci, mahukuntan ƙasar dai sun yi watsi da guguwar rashin tsaro da cin hancin da yanzu haka ke kaɗawa ,wajen buɗe bikin cika shekara guda da kafa sabuwar gwamantin shugaba Jonathan.
Tuni dai an kai ga koɗa kai da yabo a tsakanin ministocin gwamantin da suka share tsawon kusan wata guda suna bayanin irin nasarorin da gwamantin ta samu, to sai dai kuma an kai ga ƙololuwar bikin cikin rabuwar kai game da hali dama makomar da ƙasar, ke fuskanta kama daga shi kansa shugaba Jonathan da ya fito fili ya yarda ana zaman 'yan marina a tsakanin masu mulkin ƙasar ta Nijeriya.
Ba'a dada ba yana cikin labara cewar wani dan majalisar dattawan Amerika dake jamiyya daya da shugaban kasar yayi adawa da matsayin shugaban ƙasar labari ne.
Amma mu anan Nigeria in dan majalisar tarraya daga jammiyar ka ya goyi bayan ka to shine labarin ya zaa yi haka ga mu yayan jamiyya guda. Zaa ce PDP ce ta ƙasa.
Najeriya dai ta kalli wani sabon yanayin siyasar da ya mai da majalisun tarrayar ƙasar biyu wata kafa ta adawa in da kusan daukacin shekarar ta kare ga binciken badakalar cin hanci da rashawar da ma matsalar rashin tsaron da ake da ake ta'allakawa da gazawar manyan jamian gwamnatin kasar.
To sai dai kuma raba kan bai hana gwamnatin iya kaiwa ga manyan nasarorin da suka darma saa ba a cewar Mr labaran maku dake zaman ministan yada labaran kasar kuma kakakin gwamnatin:
To sai dai kuma daga dukkan alamu zaman lafiyar ne yanzu haka ke neman zama babban ƙalubalen dake ƙoƙarin wucewa da sanin gwamantin da ma jami'anta.
An dai share kusan tsawon shekara guda ana rigingimu kama daga na zare tallafin man fetur ya zuwa kasha kashen da ake ta'allaƙawa da boko haramun, sannan da satar mutanen da fashi da makamin da masu sana'ar sa ke ƙara gogewa , ban da kuma ƙaruwar fatara da talauci dama rigingimu na addinin da suka kama hanyar raba 'yan ƙasar da dama da tunanin iya kaiwa ga tudun mun tsira a cikin jirgin na shugaba Jonathan.
Dr junaid Mohammed dai na zaman shugaban Jam' iyyar PSP mai adawa:
Rawar gani ko kuma son zuciya dai sannu a hankali dai kasar ta Nigeria na neman sake fadawa cikin wani sabon rikicin mulkin da abaya ya nemi barazana ga makomar ta baki daya.
Za ku iya sauraran rahotani game da cikar shekara guda da mulkin Jonathan da wakilanmu suka aiko daga Najeriya
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Usman Shehu Usman