1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jonathan ya albarkaci kasafin kuɗin Najeriya

April 13, 2012

Bayan ɓata tsawon lokaci ana kai kawo, shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya rattaba hannu kan kasafin kuɗin ƙasar na bana.

https://p.dw.com/p/14dp9
©Jonathan Rebboah/Wostok Press/Maxppp France, Paris 25/11/2011 Le president du Nigeria Goodluck Jonathan arrive au palais de l Elysee The President of Nigeria Goodluck Jonathan at the Elysee Palace
Hoto: picture alliance / dpa

An dai kai ga alƙawuran sauyi ga rayuwar al'umma, to sai dai kuma ana shirin gannin daban ga al'ummar tarrayar Najeriya da suka share tsawon wattani kusan biyar suna jiran kasafin kuɗin ƙasar da gwamnatin ta alƙawarta kammala shi a kan lokaci.

Duk da cewar dai tun a watan Disamban bara ne dai shugaba Goodluck Jonathan ya miƙa kasafin na Naira miliyan zambar dubu huɗu da miliyan dubu bakwai sai a wannan Juma'a dai aka kai ga kammala jani in jakan kasafin da ya samu ƙarin ma'aunin dala biyu kan kowace gangar man da ƙasar ke dogaro da ita domin harkarta ta yau da kullum, da ma rikicin zargin neman ƙara yawansa a ɓangaren shugabannin ma'aikatu da hukumomin gwamantin ƙasar.

Abun kuma da ya kai ga cece kuce da ma musayar yawu a tsakanin fadar gwamantin ƙasar da shugabanta ke zargin haɗa baki wajen aringizon kasafin da kuma majalisun tarrayar biyu da suka ce babu ruwa balle tsakinsu kan batun.

Ba za a ba wa shugabannin ma'aikatu ƙarin kuɗi ba

Shugaba Jonathan ya ce zai ci-gaba da roƙon 'yan majalisa cewa duk wani shugaban ma'aikata ko hukumar gwamanti da ya zo neman ƙarin kasafin kuɗi to su kore shi. Sannan sai ya ƙara da cewa.

The Central Bank of Nigeria was established by the CBN Act of 1958 and commenced operations on July 1, 1959.[1] Governor: Sanusi Lamido Sanusi Headquarters: Abuja, Nigeria Quelle wikipedia, public domain
Ginin babban bankin Najeriya a birnin Abuja

"Kuma a bana muna fushi da hakan kuma zan yi amfani da bayyanan sirrin dake nuna wasu shugabannin ma'aikatu sun nemi ƙarin kasafi, in sallame su domin nuna misali ga kowa. Ba za mu iya tafiyar da ƙasar da babu tsari a cikin ta ba.”

Tsari ko kuma ƙoƙarin son kai dai ana yiwa batun na kasafi a tarrayar Najeriya kallon da ma ta azurta kai ga shugabannin ma'aikatu da hukumomin gwamantin da kan kai har ga ba da cin hanci domin samun kasafin da mafi yawansa ke tafiya aljihun 'yan'uwa da abokan arzuka maimakon ayyukan raya ƙasar ta Najeriya dake tsaka ga batun fatara da tashe tashen hankula.

To sai dai kuma a cewar Senata Badamasi Maccido dake zaman shugaban kwamitin kasafin majalisar dattawan Najeriya a bana ba su kai ga fuskantar irin wannan matsala ba.

Har yanzu ba ta canja zane ba

Sabon kasafin na Naira miliyan zambar dubu huɗu da miliyan dubu 690 dai ya ƙunshi kasha 28.5 cikin 100 domin manyan ayyuka da kuma kaso 78 da aka ware domin harkokin yau da kullum.

Abun kuma da ya sa masana ke masa kallon ba ta sauya zane ba ga ƙasar da shugabanta yayi alƙawarin sauyi amman kuma yawan fatara da talauci ke ƙaruwa a tsakanin al'ummarta, inji Bello Diko Ƙauran Namoda masanin harkokin tattalin arzikin ƙasar ta Najeriya.

Ngozi Okonjo-Iweala, coordinating minister for economy and finance of Nigeria, speaks during a plenary session at the 42nd annual meeting of the World Economic Forum, WEF, in Davos, Switzerland, Thursday, Jan. 26, 2012. The overarching theme of the meeting, which will take place from Jan. 25 to 29, is "The Great Transformation: Shaping New Models". (AP Photo/Keystone, Jean-Christophe Bott)
"Halin a kashe kowa ya rasa"-ministan kuɗin Najeriya Okonjo-Iweala dake neman shugabancin Bankin DuniyaHoto: dapd

Saɓa alkawari ko kuma ƙoƙarin tabbatar da daidaiton al'amura shi kansa sabon kasafin na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnati ke kukan karyewar tattalin arzikin ƙasar.

A karo na farko dai an ruwaito ministan kuɗin Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala na zargin abun da ta kira halin a kashe kowa ya rasa da abun da ta kira rushewar tattalin arzikin da Najeriyar ke fuskanta a yanzu haka. Iwealan dai ta ce asusun rarar ƙasar ta Najeriya ya koma dalar Amurka miliyan 3.6 daga kusan miliyan dubu 40 ɗin da yake shekaru kusan shida da suka gabata.

A ƙasa kuna iya sauraron rahoto kan martanin 'yan Najeriya da hira da Shehu Sani na ƙungiyar kare haƙkin ɗan Adam game da kasafin kuɗin.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Mohammad Nasiru Awal