John Magufuli ya lashe zaben shugaban kasar Tanzaniya
October 29, 2015
Hukumar zaben kasar Tanzaniya ta ce da dan takarar jam’iyya mai mulki ta CCM John Magufuli ya samu fiye da kashi 58 cikin 100, yayin da abokin karawarsa Edward Lowassa ya samu kusan kashi 39 cikin 100.