Jogoran adawan Rasha ya mutu
February 28, 2015Talla
Fitaccen mai sukar gwamnati kasar ta Rasha kana jagoran 'yan adawan kasar Boris Nemtsov, ya rasu bayan harbe shi da aka yi a birnin Moscow. Daya daga cikin mutanen da aka sani kan sukar shugaba Vladimir Putin, an harbe shi ne a daren jiya Juma'a a kusa da fadar Kremlin. An dai bayyana cewa wanda ya hallaka Nemtsov ya harbe shi ne har sau hudu. Nan take dai shugaba Putin ya yi Allah wadai da kisan, kana ya bukaci a gudanar da bincike don gano wadanda suka hallaka babban abokin adawara ta sa.