1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kayan agaji ya isa yankin Aden na Yemen

Yusuf BalaJuly 21, 2015

Jirgin da ke zama na shirin abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya isa gabar tekun Aden bayan jira na tsawon kimanin makwanni hudu.

https://p.dw.com/p/1G29L
Iranische Kriegsschiffe am Golf von Aden
Jirgin soja na tunkarar gabar tekun AdenHoto: Irna

Dakarun sojan kasar Yemen da ke samun goyon bayan Saudiyya na daf da kwace garin Aden da ke Arewacin kasar baki daya daga hannun mayakan Houthi da ke zama gari mai muhimmanci a garesu a kan gaba.

Wannan kasa ta Yemen da mayakan na Houthi ke cin karansu babu babbaka na musayar makaman atilare da dakarun sojan kasar da ke samun goyon bayan Saudiyya a garin Dar Saad da al Alam inda jiragen sojojin kawancen Larabawa suka yi ruwan bama-bamai kan mayakan na Houthi masu samun goyon bayan Iran.

A wani labarin kuma a ranar Talatan nan ce wani jirgin shirin abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya isa gabar tekun Aden bayan jira na tsawon kimanin makwanni hudu. Wannan jirgi dai na dauke da kayan abinci ne da ake saran za a yi amfani da su wajen ciyar da kimanin mutane 180,000.

Garin dai na Aden da ma wasu larduna da ke kudancin kasar ta Yemen sun kasance wuri da ke da wahalar shiga dan kai agaji ga kimanin mutane miliyan 13 sama da yawan adadin al'ummar kasar wadanda suke cikin hali na matsananciyar bukata.