1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsokaci kan siyasar Angola a Jaridun Jamus

Usman Shehu Usman LMJ
September 16, 2022

Siyasar Angola da batun yarjejeniyar Jamus da Namibiya kan kiyashi da riga-kafin zazzabin cizon sauro wato malaria, sun dauki hankulan jaridun Jamus na wannan makon.

https://p.dw.com/p/4Gzd4
Angola Luanda | Shugaba João Lourenço
An sake rantsar da Shugaba João Lourenço a wa'adi na biyu a AngolaHoto: Julio Pacheco Ntela/AFP/Getty Images

A sharhinta na wannan mako, jaridar die Tageszeitung cewa ta yi, kasar Angola na cikin wani yanayi mai hadari bayan zabukan da ke cike da tababa. Jaridar ta ce Angola dai na cikin tsaka mai wuya, bayan takaddama ta kunno kai dangane da sakamakon zaben da aka gudanar a karshen watan Agusta. Kasar wacce jam'iyyar MPLA ke mulki tun bayan samun 'yancin kai daga kasar Portugal a shekarar 1975, za ta iya shiga wani sabon yanayin dimukuradiyya mai jam'iyyu da dama kamar yadda za a iya sake komawa cikin danniya ta mulkin kama-karya. Masharhanta na cewa ya kamata hukumomin Angola, su sanya tsari na zahiri domin bin cikakkiyar dimukuradiyya.
Jaridar Neues Deutschland kuwa a sharhinta cewa ta yi, 'yan adawar Namibiya na son sake tattaunawa kan yarjejeniyar kisan kare dangi na Herero da Nama. Gwamnatin Jamus na adawa da wannan mataki, abin da ya janyo bacin rai a Namibiya. Yayin yarjejeniyar da aka gabatar a watan Mayun shekarar da ta gabata ta 202, an shirya samun daidaito kan biyan diyya sakamakon kisan kiyashin da sojojin Jamus suka yi tsakanin shekara 1904 zuwa 1908 a Herero da Nama lokacin da Jamus din ta yi mulkin mallaka a Kudu maso Yammacin Afirka.

Namibia | Zanga-zanga | Kisan Kiyashi | Jamus | Diyya
Al'ummar Namibiya na fatan sake tattaunawa da Jamus, kan batun kisan kiyashiHoto: Hitradio Namibia
Riga-Kafi | Zazzabin Cizon Sauro | Malaria
Kyakkyawan fata kan allurar riga-kafin zazzabin cizon sauro wato malariaHoto: Joseph Oduor/AP Photo/picture alliance

Jaridar Süddeutsche Zeitung kuwa na cewa: za a iya samun riga-kafin cutar zazzabin cizon sauro nan gaba kadan, bayan da aka tabbata da cewa riga-kafin ta yi tasiri sosai a kan cutar. Masu binciki na saran za a iya amincewa da ita a farkon shekara mai zuwa ta 2023. Masani Oxford Adrian Hill da sauran masu bincike daga Birtaniya da Burkina Faso, sun fitar da bayanai da ke nuni da cewa tasirin riga-kafin da ake kira da R21 da aka gwada ya kai kaso 80 cikin 100.