1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Libiya da Mali cikin jaridun Jamus

Usman Shehu Usman LMJ
July 7, 2023

Zaben Senegal da hari a kan sansanin sojojin hayar Rasha na Wagner a Libiya da janye dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Mali, sun dauki hankulan jaridun Jamus na wannan makon.

https://p.dw.com/p/4TbWZ
Zabe | Senegal | Macky Sall | Shugaban Kasa | Tazarce
Shugaban Senegal Macky Sall ya yi bankwana da tazarceHoto: Lewis Joly/AP/picture alliance

Jaridar die tageszeitung ta ce Shugaba Macky Sall na kasar Senegal ya bayyana cewa ba zai sake tsayawa takara a zaben shugaban kasar da ke tafe ba. Sall din ya ceto kasarsa cikin rikici, a zaben da za a gudanar a watan Fabrairun shekara ta 2024 da ke tafe. Matakin nasa na zuwa ne, makonni hudu kacal da yanke hukunci mai cike da cece-kuce da aka yi ga madugun 'yan adawar kasar Ousmane Sonko da ya haifar da zanga-zangar da ta yi sanadiyar mutuwar mutane da dama. Kallon da ake wa Senegal a matsayin kasar da ake gudanar da dimukuradiyya mafi inganci a yammacin Afirka ya kau, sakamakon tarzoma da tashe-tashen hankula sakamakon kokarin jami'an 'yan sanda na murkushe masu zanga-zanga da karfin tuwo.

Libiya | Yaki | Hari | Wagner
Kkasar Libiya dai ta jima cikin halin yaki da tashe-tashen hankulaHoto: Imago

Ita kuwa jaridar der Tagesspiegel ta rubuta sharhinta tana mai cewa: A karshen makon jiya an kai farmaki kan sansanin sojojin haya na Rasha na kungiyar Wagner da ke Libya. Jaridar ta ce an kai harin ne tare da jirage marasa matuka, sai dai babu dai rahoton mutuwa a bangaren sojojin hayar na Wagner. Ko Amurka ce ke da alhakin harin? Da ma an kai makamancin wannan harin a cikin watan Janairu tare da lalata jirgin yakin Rasha, a wancan lokaci jaridar "Washington Post" ta ce Amurka ce ta kai farmakin. Gwamnatin Libiya ta tabbatar da afkuwar sabon harin, sai dai ba a san wanene ke da alhakin kai shi ba.

Mali | MINUSMA | Dakaru | Wanzar da Zaman Lafiya | Majalisar Dinkin Duniya
Shirin janye dakarun MINUSMA na Majalisar Dinkin Duniya daga MaliHoto: Loey Felipe/UN/dpa/picture alliance

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung kuwa ta mayar da hankali ne kan matakin janye Rundunar Wanzar da Zaman Lafiya na Majalisar Dinkin Duniya wato MINUSMA daga Mali. Jaridar abin fargabar shi ne yadda abubuwa za su ci gaba da wakana a kasar, bayan kawo karshen aikin rundunar ta Majalisar Dinkin Duniya a Mali. Koda yake jagoran juyin mulkin kasar kana shugaban gwamnatin rikon kwaryar soja Assimi Goita ya bukaci al'ummar Malin da su goyi bayansa, a kan abin da ya kira kokarin ceto kasar da zai zame musu matakin samun kwanciyar hankali dama kare kasar. Ya kuma bukaci al'ummar Malin da su ci gaba da yin addu'o'i, domin tabbatar da dawowar zaman lafiya mai dorewa a kasar.