Jaridun Jamus: Rikicin Gambiya da yaki da ta'adda a Najeriya
January 20, 2017A labarin da ta buga game da kasar Gambiya jaridar Neues Deutschland ta fara ne da cewa:
A ranar 19 ga watan Janairu wa'adin mulkin Shugaba Yahya Jammeh da ya sha kaye a zabe, ya kawo karshe amma ya ki mika mulki ga mutumin da ya yi nasara a zaben na watan Disamban 2016 wato Adama Barrow wanda ya bar kasar zuwa makwabciyar kasa Senegal kuma har ya sha rantsuwar kama aiki a ofishin jakadancin Gambiyar da ke birnin Dakar a ranar Alhamis. Su kuma a na su bangaren kasashe makwabta na kungiyar ECOWAS sun shirya tsaf na aiwatar da barazanar tura dakarun soji don su fatattaki Jammeh da ya shafe shekaru 22 kan karagar mulki. Tuni dai Jammeh wanda ministocinsa ke ta yin murabus ya ayyana dokar ta-baci ta tsawon watanni uku.
Kuskuren matuki ya janyo asarar rayuka
Ruwan bama-bamai a kan sansanin ‘yan gudun hijira a Najeriya babban kuskure na matukin jirgin saman yaki da ya yi sanadiyyar rayuka da yawa, inji jaridar Neue Zürcher Zeitung.
Ta ce maimakon kai hari kan maboyar Boko Haram, sojin saman Najeriya bisa kuskure sun yi lugudan bama-bamai kan wani sansanin ‘yan gdun hijira da suka tsere daga ta'asar mayakan Boko Haram a kauyen Rann na jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya. Kimanin mutane 70 ciki har da ma'aikatan agaji suka rasa rayukansu a harin. Jaridar ta ce wannan dai ba shi ne karo na farko da sojojin Najeriyar bisa kuskure suka kai hari kan fararen hula ba, amma ana iya cewa shi ne karon farko da wani shugaban Najeriya ya fito fili ya amsa tabka irin wannan kuskure.
Gagarumin shirin tallafa wa Afirka
Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung a wannan makon sharhi ta yi kan sabon gagarumin shirin tallafa wa nahiyar Afirka da aka yi wa lakabi da „Marshall Plan" da gwammatin Jamus ta gabatar a wannan makon.
Ta ce ministan kula da ayyukan raya kasashe masu tasowa na Tarayyar Jamus Gerd Müller ya kuduri aniyar kulla huldar cinikaiya ta adalci da kasashen Afirka, da zai duba muradun bangarorin biyu. Shirin na da burin kawar da duk wasu ababe da ke kawo tarnaki ga huldar cinikaiya da saka jari a tsakanin Jamus da kasashen na Afirka tare kuma da karfafa yaki da talauci tun daga tushe, matakin da a cewar jaridar yana da muhimmanci sosai har ga kasashe masu karfin tattalin arziki kamar irin su Jamus, wadanda ke kokarin dakile kwararowar bakin haure daga kasashen Afirka.