Tarzoma a Yuganda da boren adawa da gwamnatin Burkina Faso
November 19, 2021A yau za mu fara sharhin jaridun na Jamus kan nahiyarmu ta Afirka da kasar Yuganda, inda aka samu fashewar bama-bamai. Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta yi sharhi tana mai cewa an samu karuwar alkaluman wadanda harin ya shafa. Sannan ta kara da cewa bayan harin ta'addanci da aka kai a Kampala babban birnin kasar Yuganda, yanzu alkaluman wadanda suka mutu ya kai mutane 13, yayin da kimanin mutane 30 suka jikkata. A wannan Talata ce aka samu harin ta'addancin. Gwamnati ta ce kawo yanzu an kama kimanin mutane 80 da ake tuhumarsu da alaka da kungiyar da ake zargi da kai harin. Gwamnatin Yuganda dai na zargin kungiyar 'yan tawaye ta ADF da kai harin.
Har yanzu muna kan batun ta'addanci, amma a wannan karo ba hari ne aka kai ba, amma 'yan kasa ne ke kokarin kare kansu. Jaridar Die Tageszeitung ce ta yi labarin daga kasar Burkina Faso, inda aka kaddamar da wata kungiya da ta fara yin bore kan gwamnatin Burkina Faso tana mai cewa sun gaji da yadda aka jima ana kisan jama'a amma hukuma ta kasa yin wani abu don kare su.
Su ma dai jam'iyyun adawar kasar sun yi kira da shugaban kasar ta Burkana Faso ya sauka daga mulki. Fararen hula kimanin 300 da suka fusata suka hau kan tituna dauke kwalaye da sauransu. Yanzu dai an yi kiyasin kimanin 'yan kasar miliyan daya da rabi ne suka tsere daga rikicin da ke faruwa a yankin da 'yan ta'adda suka fi karfi.
Idan muka leka jaridar Handelsblatt wacce ke rubuta labarai kan tattalin arziki da hada-hadar kasuwanci, ta bayyana cewa, annobar Corona ta jawo rarrabuwar kawunan 'yan siyasa da kamfanoni, inda jaridar ta ce manyan kamfanonin ba da rance a yanzu ba a cika yin maraba da su a kasashen Afirka ba. Jaridar ta ba da misali da kasar Saliyo. Ta ce kasar ta Saliyo, wacce ta yi fama da yakin basa a baya, a yanzu kuma ta fada wani sabon rikici na tattalin arziki. Sai dai yanzu haka ta cimma yarjejeniya da kasar China da za ta gina sabuwar tashar jiragen ruwa don karfafa harkar kamun kifi, da akalla za ta bude damar yin kasuwa ga masu kamun kifi da samar da guraben aikin yi ga jama'ar kasar ta Saliyo.
Yanzu kuma za mu duba jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, wacce ta yi tsokaci kan matsalar sauyin yanayi. Jaridar ta fara ne da aza ayar tambaya, wai shin za a iya kare tekuna a duniya? Kuma wacce rawar bangaren yawon shakatawa zai taka in har ana son tekuna da ake da su a duniya. Misali tsibirin Benguerra da ke a gabar ruwan kasar Mozambik, inda wasu daidaikun mutane ne a wannan tsibirin kasar Mozambik, ita ce kare hallitun ruwa. Wasu likitoci da suka kware kan hallitun ruwa, sune ke gudanar da aikin, da nufin ragen irin hatsari da dabbobin ruwa ke fuskanta.