Janye sojan Faransa a Nijar
October 5, 2023Talla
Kusan makwanni biyu da suka gabata ne dai shugaba Emmanuel Macron, ya yi amayi ya lashe inda ya sanar da janye dakarun kasar da ma jakadan Faransa dake Jamhuriyar Nijar, wanda a baya Faransa ta yi kememen cewa gwamnatin sojan Nijar ba ta da halarci don haka ba ta da izinin hana Faransa zama cikin kasar ta. Faransa dai na da sojoji kimanin 1500 da ke Nijar, wanda ke wajen don su yaki ta'addanci, amma a cewar sabuwar gwamnatin Nijar, sojojin na Faransa ba sa tabuka komai, don haka ba a bukatarsu. Inda maimakon kungiyar G5 Sahel wace Faransa ta jogoranci kafawa, kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar wadanda duk suka kori sojojin Faransa daga kasashensu, sun kafa wata sambuwar kungiya ta kawancen tsaro a yankin na Sahel.