Rasha: An yi jana'izar jagoran 'yan adawa Navalny
March 1, 2024Talla
Mai magana da yawun fadar Kremlin Dmitri Peskov ya gargadi jama'ar da su kiyaye yin amfani da damar domin yin zanga-zanga ba tare da izini ba. Babban mai sukar lamirin gwamnatin kuma mai fafutukar yaki da cin hanci da rashawa, Alexeï Navalny ya mutu a ranar 16 ga Fabrairu yana da shekaru 47 a wani yankin Rasha da ke yankin Arctic a cikin wani yanayi da ba tantance ba har yanzu. Kusan mutane 400 ne 'yan sanda suka kama a kwanakin da suka biyo bayan mutuwarsa a yayin gudanar da gangamin da aka tsara domin tunawa da shi.