Jamusawa za su sami rangwamen haraji
November 7, 2011Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta shaidawa manema labnarai cewar da yammacin Lahadin nan ne aka cimma yarjejeniya tsakanin jam'iyyar ta ta CDU da kuma sauran jam'iyyun da take ƙawance tare da su game da yiwa Jamusawa rangwamen harajin da zai kai na kuɗi Euro miliyan dubu shidda cikin tsukin shekaru biyu, farawa daga shekara ta 2013. Merkel ta bayyana matakin da cewar godiya ce ga Jamusawa bisa namijin ƙoƙarin da suka yi wajen nuna juriya ga ɗaukar ɗawainiyar rikicin tattalin arziƙin da wasu ƙasashen Turai ke fama da shi a yanzu haka.Sai dai kuma ta ce akwai ƙarin ayyukan da ke gaba.
Shugabar gwamnatin Jamus ɗin ta ce a cikin watan Janairun 2013 ne za'a fara aiwatar da shirin yin ragin harajin na kuɗi Euro miliyan dubu biyu daga ƙanana da kuma matsaƙaitan masu samun kuɗaɗen shiga. A cikin watan Janairun 2014 ne kuma za'a rage kaso na biyu na harajin, wanda shi kuma zai kai na kuɗi Euro miliyan dubu huɗu. Sai dai ba za'a fara ɗaukar matakin ba, har sai majalisar dokokin Jamus ta zartar da doka akan hakan.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Halima Balarabe Abbas