1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus zata goyawa sabon babban sakataren MDD Ban Ki-Moon baya

December 8, 2006
https://p.dw.com/p/BuYq

SGJ Angela Merkel ta yi alkawarin cewa Jamus zata ba da cikakken goyon baya ga sabon sakatare janar na MDD Ban Ki-Moon, tana mai jaddada bukatar da ke akwai ta ci-gaba da yiwa majalisar canje canje. A gun wata ganawa a birnin Berlin Merkel ta ce sabon babban sakataren na da jan aiki a gabansa. Merkel ta kara da cewa gwamnati a Berlin zata matsa kaimi don kara yawan membobin kwamitin sulhu. A nasa bangaren Mista Ban ya yabawa Jamus dangane da gudunmawar da take bawa MDD musamman a ayyukan samar da zaman lafiya da tabbatar da manufofin kare hakin dan Adam. A ranar daya ga watan janeru na shekara ta 2007 mista Ban dan kasar KTK zai maye gurbin Kofi Annan a matsayin shugaban Majalisar ta Dinkin Duniya.