Gyaran dokar zabe don rage wakilan majalisa
August 26, 2020Talla
Bayan tsawon lokaci ana tafka muhawara, jam’iyyar CDU ta shugabar gwamnati Angela Merkel da takwararta ta CSU da kuma SPD dukkaninsu sun amince da wasu matakai biyu da za a fara aiwatarwa a shekara mai zuwa domin rage yawan mazabu daga 299 zuwa 280 kafin zaben da za a gudanar a shekara ta 2025.
Matakin a cewar shugabar jam’iyyar CDU Annegret Kramp-Karrenbauer, ana fatan zai taimaka wajen rage yawan wakilai a majalisar dokokin.
A halin da ake ciki majalisar wakilan ta Bundestag ta na da yawan 'yan majalisa 709 inda ta kasance majalisa mafi yawan wakilai. Majalisar da ta fi ta yawan wakilai ita ce majalisar dokokin China wadda ke da yan majalisa 2980.