Shugaban Jamus ya kammala ziyarar aiki a Afirka
November 21, 2018Talla
Shugaban ya tabo batutuwa da suka kunshi yaki da cutar HIV da matsalar fari da sauyin yanayi ke haifarawa. Wannan ziyarar wani tubali ne na ingantuwar dangantaka tsakanin kasashen biyu.
Daga shekara ta 2019 Afirka ta Kudun da Jamus za su cigaba da zama membobi a kwamitin sulhu na MDD, dangane da haka ne Steinmeier ya bayyana alakar kasashen biyu a matsayin abu mafi dacewa.Baya ga Afirka ta Kudu, Steinmeier ya ziyarci kasar Botswana.