Merkel ta yarda ga shirin sake tsaraTurai
June 3, 2018Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta sanar da amincewa da shirin shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron na sake fasalin tsarin tafiyar Turai ta yadda kasashen nahiyar za su iya sake inganta tattalin arzikinsu a lokacin da Birtaniya za ta kammala shirinta na ficewa daga kungiyar EU. Merkel ta sanar da matsayin nata ne a wata fira da ta yi da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung.
Shirin na Shugaba Macron ya tanadi samar da wani kasafin kudi a tsakanin kasashen na EU da zimmar taimakon juna ta hanyar saka jari da kuma samar da bashi ga kasashen nahiyar da za su fuskanci matsalar tattalin arziki.
Watanni da dama kenan dai da Shugaba Macron na Faransa ke neman hadin kan Jamus a cikin wannan shiri nasa, amma shugabar gwamnatin ta Jamus na nokewa a bisa fargabar da take ta ganin shirin ya bukaci tallafin kudi daga kasar ta Jamus wacce ke zama mafi karfin tattalin arziki a nahiyar ta Turai.