1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Shekaru 25 bayan rikicin kyamar baki

Mohammad Nasiru Awal RGB
August 22, 2017

A ranar 22 ga watan Agustan shekarar 1992 birnin Rostock da ke gabacin tarayyar Jamus ya kasance wani dandalin tashin hankali mafi muni kan baki a Jamus tun bayan yakin duniya na biyu.

https://p.dw.com/p/2ie7P
Ausschreitungen Rostock Lichtenhagen 1992
Hoto: picture-alliance/ZB/B. Wüstneck

Mazauna birnin sun yi wa wata cibiyar tsugunar da masu neman mafakar siyasa dirar mikiya inda suka mamaye cibiyar tsawon kwanaki a unguwar Lichtenhagen da ke a birnin na Rostock na gabacin Jamus. Shekaru 25 da suka wuce aka bude cibiyar tsugunar da masu neman mafakar siyasa duk da haka hukuma ta gaza yin tanadin wuraren tsabta ga daruruwan 'yan Roma da Sinti da aka tsugunar a cibiyar, abin da ya mayar da wurin wani juji.

Ausschreitungen Rostock Lichtenhagen 1992
Wasu daga cikin bakin da aka kwashe daga gidan da aka kai ma hari a ranar 22 ta Agustan 1992Hoto: picture-alliance/dpa/B. Wüstneck

Bayan da gwamnati ta ki sauraron koke-koken jama'a, da maraicen ranar 22 ga watan Agustan shekarar 1992 mazauna unguwar sun dauki doka a hannu inda suka farma gidan da aka zaunar da bakin. 'Yan sanda kalilan da aka tura don kare bakin su ma an kai musu hari, abin da ya suka tsere. Sai can cikin dare sannan aka kai karin jami'an tsaro da suka yi amfani da feshin ruwa kan masu kyamar bakin. Washegari masu kyamar bakin sun samu dauki daga kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayin kyamar baki da suka tashi daga wasu garuruwan Jamus zuwa Rostock. Mutane kuwa suka yi ta sowa da zarar an jefa bam din fetir cikin gidan. An dai kwashe masu neman mafakar siyasa daga gidan amma an bar 'yan asalin kasar Vietnam su 120 ciki har da kananan yara a wani gidan da ke kusa inda su din ma aka kai musu hari.

Abubuwa dai sun sauya tun bayan aukuwar lamarin shekaru 25 da suka wuce amman zuwa wannan lokacin batun kyamar baki abu ne da ke daukar hankali musamman a gabacin Jamus. A bara yawan hare-hare masu nasaba da masu kyamar baki ya karu a Jamus, lamarin da ya sa masharhanta suka ce da sauran aiki a gaba.